Hukuncin Kotu 5 da Suka Girgiza Kowa a Shari’ar Zaben Gwamnoni Da ‘Yan Majalisa

Hukuncin Kotu 5 da Suka Girgiza Kowa a Shari’ar Zaben Gwamnoni Da ‘Yan Majalisa

  • Kusan babu shari’ar da ta dauki hankalin mutane sosai irinta Abba Kabir Yusuf v Nasiru Yusuf Gawuna a zaben jihar Kano
  • Abubakar Ohere (APC) ya rasa kujerar sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a hannun Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP)
  • Jam’iyyar PDP ta rasa mukamai masu yawa a Filato, mutane sun zura idanu domin ganin hukuncin shari’ar zaben gwamna

Abuja - Bayan an ayyana wadanda su ka yi nasara a zaben 2023, kotu suna cigaba da yanke hukuncin kararrakin da aka gabatar masu.

A rahoton nan, abin da mu ka yi shi ne tattaro hukuncin zaben da suka bada mamaki a neman takarar Gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya.

Zaben 2023
Was shar'io'in zaben 2023 da su ka bada mamaki Hoto: Abba Kabir Yusuf, Natasha Akpoti-Uduaghan, thesparklightng.com
Asali: Facebook

1. Abba Kabir Yusuf

Kamar yadda lauyan Abba Kabir Yusuf ya fada, wannan ne karon farko da za a rusa nasarar zabe saboda rashin hatimi, sa hannu da kwanan wata.

Kara karanta wannan

Abba v Gawuna: Abubuwa 12 da Kotun Daukaka Kara Za Ta Duba a Shari'ar Zaben gwamnan Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin haka aka sokewa NNPP kuri’u fiye 165, 000, kotun korafin zabe ta ce Nasiru Yusuf Gawuna ne halattaccen wanda ya ci zaben gwamnan Kano.

2. Natasha Akpoti-Uduaghan

Da aka je kotu Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi nasarar karbe kujerar Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa a hannun jam’iyyar APC.

Abin da ya fi daukar hankali shi ne ganin Natasha Akpoti-Uduaghan mace ce da ta yi nasara a karkashin PDP a mazabar da Gwamna Yahaya Bello ya fito.

3. Simon Lalong

BBC ta ce babban abin da aka fi damuwa da shi yanzu shi ne matakin da Simon Lalong zai dauka da kotu ta ce Ministan ne Sanatan Filato ta kudu.

Sauran shari’o’in zaben jihar Filato sun bada mamaki ganin yadda jam’iyyar PDP ta rasa kujeru bakwai a majalisa, mukamanta sun koma hannun APC da LP.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun daukaka kara ta sake yanke hukunci kan zaben Majalisar Tarayya, ta yi bayani

4. Elisha Abbo

Sanata Elisha Abbo ya fuskanci kalubale iri-iri a zaben Sanatan Adamawa ta Arewa, sai a kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a Abuja, aka kawo karshensa a 2023.

Babban kotun ta ce Rabaren Amos Yohanna ne wanda ya ke da rinjayen halatattun ƙuri'u. hakan ya kawo karshen Sanatan da ya yi suna a majalisar dattawa.

5. Darlington Nwokocha

Ana da labarin yadda kotu soke nasarar Sanata Darlington Nwokocha (LP), ta ce Kanal Austin Akobundu (PDP) ne Sanatan Abia ta tsakiya a majalisa.

Sai dai zanga-zanga ta barke saboda magoya bayan LP ba su ji dadin hukuncin ba, an ji PDP ta na cewa an bi ta bayan fage a dawo da Sanatan da aka sauke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng