Jam’iyyar APC Ta Hurowa Kotu Wuta Za a Canza Hukuncin Nasarar Sanatanmu Inji PDP
- Kotun daukaka kara ta dawo ta ayyana Kanal Austin Akobundu mai ritaya a matsayin Sanatan Jihar Abia ta tsakiya
- Jam’iyyar PDP ta ce bayanai sun zo mata cewa jam’iyyar APC ta biyo ta bayan fage, yanzu ana so a canza hukuncin kotun
- Debo Ologunagba ya zargi Sanatan jam’iyyar LP da aka tsige, Darlington Nwokocha da shirin sauya sheka zuwa APC
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babban Jam’iyyar hamayya ta PDP ta fara kokawa cewa akwai kutun-kutun da ake yi domin karbe mata kujera a majalisar dattawa.
Vanguard ta ce jawabi ya fito daga ofishin Sakataren yada labaran PDP, ana zargin APC da kitsa yadda za a hana Austin Akobundu shiga ofis.
Jam’iyyar ta PDP ta ce ana so ayi amfani da kotun daukaka kara, a raba Sanata Austin Akobundu daga kujerarsa bayan an ba shi gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hukuncin da aka yi, babban kotun ta tabbatar da cewa Kanal Austin Akobundu mai ritaya ne zababben Sanatan yankin Abia ta tsakiya a 2023.
Daga baya kuma, PDP ta ce an dawo ana so a canza hukuncin da aka yi a babban kotun da ke garin Legas, a ce an yi kuskure wajen shari’ar.
PDP: Jawabin Debo Ologunagba
"Ba sabon labari ba ne kotun daukaka kara mai zama a Legas ta soke nasarar Darlington Nwokocha na LP a matsayin Sanatan Abiya ta tsakiya.
Kamar yadda aka sani, hukuncin kotun ya jawo farin ciki ya barke ba a Abia ta tsakiya kadai ba, a duk fadin jihar Abiya da bangarorin Najeriya.
Sai dai kuma jam’iyyarmu ta PDP ta bankado wani shiri da wasu jagororin APC su ke yi na matsawa kotun daukaka karar ta canza hukuncin da ta yi.
A janye hukuncin da aka yi na cewa Kanal Austin Akobundu(rtd) ne halataccen Sanata.
Mun samu labari an hurowa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wuta ya yi watsi da hukuncin kotu, ya ki rantsar da Austin Akobundu."
- Debo Ologunagba
Jam’iyyar ta kara da zargin Darlington Nwokocha da hada-kai da APC cewa zai sauya-sheka zuwa jam’iyya mai mulki idan ya rike kujerarsa.
Shari'ar APC v NNPP a zaben Kano
Rahoto ya nuna Nasiru Gawuna ya dauko tsohonMinistan shari'a, Akinlolu Olujinmi, SAN domin ya karbar masa mulkin Kano a Kotun daukaka kara.
Akinlolu Olujinmi, SAN da Wole Olanipekun, SAN suke karawa wajen daukaka karar shari’ar Kano, dayan lauyan shi yake kare Abba Kabir Yusuf.
Asali: Legit.ng