Sabon rikici ya bulla a PDP, EFCC ta na farautar wasu shugabannin Jam’iyya 3 a kan satar N10bn

Sabon rikici ya bulla a PDP, EFCC ta na farautar wasu shugabannin Jam’iyya 3 a kan satar N10bn

- EFCC ta yi aiki a kan korafin da aka gabatar a kan Shugabannin PDP

- Kazeem Afegbua ya na zargin PDP-NWC da batar da makudan kudi

- Hukumar EFCC ta gayyaci wasu jami’ai, za ayi masu tambayoyi yau

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta gayyaci jami’an jam’iyyar PDP domin ta yi masu wasu tambayoyi.

Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP da laifin sata, karkatar da kudi, kutun-kutun da hannu wajen laifi.

Hakan na zuwa ne bayan jigon jam’iyyar hamayyar, Kazeem Afegbua, ya gabatar da korafi gaban EFCC, ya na neman a binciki Price Uche Secondus.

KU KARANTA: Shugaban PDP zai kai kara kotu bayanana zarge shi da lakume N10bn

A wata takardar gayyata da hukumar EFCC ta aikowa Prince Uche Secondus a ranar 17 ga watan Mayu, 2021, ta bukaci jin wasu bayanai daga bakinsu.

EFCC ta nemi shugaban jam’iyyar ya bada aron shugaban mai binciken kudi, da babban sakataren gudanarwa, da dakretan kudi zuwa hedikwatar EFCC.

Wadannan jami’ai da aka nema za su bayyana a babban ofishin hukumar ta EFCC da ke garin Abuja ne tsakanin ranar 19 zuwa 21 ga watan Mayu, 2021.

A wannan wasika, EFCC ta bukaci shugabannin jam’iyyar PDP na kasa su hallara dauke da duk wasu muhimman takardu da suke da alaka da sayen fam.

KU KARANTA: Gwamnan Imo ya tsane ni haka kurum, na rasa dalili - Okorocha

Sabon rikici ya bulla a PDP, EFCC ta na farautar wasu shugabannin Jam’iyya 3 a kan satar N10bn
Uche Secondus Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Kamar yadda Kazeem Afegbua ya bukata, za ayi bincike na a kan kudin da aka samu daga saida fam din takara tun daga watan Junairun 2017 har zuwa yau.

Kazeem Afegbua ya na ganin akwai alamar tambaya a kan aikin majalisar Prince Uche Secondus.

Wadanda ake sa ran gani a ofishin EFCC daga yau zuwa ranar Juma’a sune: Kanal Austin Akobundu mai ritaya, Adamu Mustafa, da Abdullahi Maibasara.

A game da yajin-aikin da ake yi a jihar Kaduna, an ji cewa Gwamnonin APC sun fadi abin da ya kamata Gwamnatin Nasir El-Rufai da ‘Yan kwadago su yi.

Gwamnonin ta bakin shugabansu, Sanata Atiku Abubakar Bagudu, sun tsoma baki kan yajin-aikin, sun bukaci a sake zama a kan tebur domin ayi sulhu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel