Ajaero: Ka da Ku Kuskura Ku Matso Kusa da Ma'aikata Ta, Ministan Tinubu Ya Tura Gargadi Ga NLC

Ajaero: Ka da Ku Kuskura Ku Matso Kusa da Ma'aikata Ta, Ministan Tinubu Ya Tura Gargadi Ga NLC

  • Festus Keyamo, Ministan Sufurin jiragen sama ya tura gargadi mai tsauri ga kungiyar NLC kan matsalar da ake fama da ita
  • Keyamo ya gargade su da kada ta kuskura ta matso kusa ma'aikatarsa ta sufuri inda ya ce ba ya goyon bayan abin da aka yi wa Ajaero
  • Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar NLC ta mamaye filayen tashi da saukar jiragen sama a yau a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya, Festus Keyamo ya gargadi Kungiyar Kwadago a Najeriya, NLC kan kawo cikas a harkar sufuri.

Keyamo ya yi wannan gargadin ne yayin taron ma'aikatar a Effurun da ke karamar hukumar Evwie a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Keyamo ya gargadi kungiyar NLC kan mamayar filin jirgin sama
Keyamo ya yi martani kan mamayar filin jirgin sama da NLC ta yi. Hoto: Festus Keyamo.
Asali: Facebook

Wane gargadi Keyamo ya yi wa NLC?

Ministan ya yi Allah wadai da cin zarafin shugaban kungiyar, Joe Ajaero da aka yi, The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya yi gargadi kan cewa dole kungiyar ta guji kawo tarnaki a harkar sufurin kasar.

Ya ce:

"Harkar sufuri ba ta shafi cin zarafin shugaban kungiyar, Joe Ajaero ba, ku fita daga idon harkar sufuri.
"Idan aka samu matsala a harkar sufuri, hakan zai shafi 'yan kasashen ketare, ku na lalata harkokin kasar nan."

Wane shawara Keyamo ya bai wa NLC?

Ya Kara da cewa:

"Ka da ku bari jam'iyyar LP ta ruguza mu ku kungiya, ya kamata ku yi zama da shugabanninku."

Keyamo ya ce bai kamata su hada kai da jam'iyyar LP ba saboda su tafiyarsu daban ce, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Tsoma Baki a Rigingimun Dauda/Matawalle da BUA/Dangote

Ya kara da cewa wannan abin da su ke yi duka siyasa ce, ba wai tafiyar neman 'yancin ma'aikata su ke yi ba, siyasa ce zalla.

Kungiyar NLC ta mamaye filin jirgin saman Abuja

A wani labarin, kungiyoyin TUC da NLC sun mamaye filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke birnin Tarayya Abuja.

Kungiyoyin sun mamaye filin jirgin ne a yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba don yin zanga-zanga.

Wannan na zuwa ne bayan cin zarafin shugabansu, Joe Ajaero a Owerri babban birnin jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.