INEC Ta Fitar da Jerin Rumfunan Zabe 40 da Ba Za a Yi Zabe a Jihar Imo Ba, Ta Bayyana Dalili

INEC Ta Fitar da Jerin Rumfunan Zabe 40 da Ba Za a Yi Zabe a Jihar Imo Ba, Ta Bayyana Dalili

  • INEC ta bayyana cewa ba za a gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe 40 a jihar Imo ba yayin zaben gwamnan jihar da za a yi ranar Asabar
  • Hukumar zaben ta cigaba da cewa hakan ya faru ne saboda babu masu kaɗa ƙuri’a da suka yi rajista daga rumfunan zaɓen da abin ya shafa
  • Daga nan ne INEC ta bayyana cewa ba za a tura jami'an zaɓe da kayayyakin zaɓe zuwa rumfunan ba, a yayin zaɓen ranar Asabar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen rumfunan zaɓe guda 40 da ba za a gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba a jihar Imo ba.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: Abubuwa 2 da Atiku zai fara yi bayan rashin nasararsa ga Shugaba Tinubu

A cewar hukumar a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, dalilin da ya sa ta ɗauki matakin shi ne saboda babu masu kaɗa ƙuri’a a rumfunan da abin ya shafa.

Ba za a yi zabe a rumfunan zabe 40 ba a jihar Imo
INEC ta bayyana rumfunan zabe 40 da ba za a yi zaben gwamnan jihar Imo ba Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

INEC ta bayyana dalilin da ya sa ba za a yi zaɓe a rumfunan zaɓe 40 a Imo ba

Daga nan sai hukumar zaɓen ta sanar da masu ruwa da tsaki da sauran al'ummar jihar da su san halin da ake ciki, ta kuma ƙara da cewa ba za a tura jami'an zaɓe zuwa rumfunan zaɓen ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saƙon na cewa:

"Ya ku ƴan jihar Imo, da fatan za a lura cewa ba za a yi zaɓe ba a cikin waɗannan rumfunan zaɓe (kamar yadda aka maƙala a cikin hoto na 1 & 2) waɗanda ba su da masu kaɗa ƙuri'a."

Kara karanta wannan

Datti Baba-Ahmed abokin takarar Obi ya bukaci Tinubu da Shettima su yi murabus, ya bayyana dalilansa

"Kada ku yi tsammanin zuwan ma'aikata da kayayyakin zaɓe a waɗannan wuraren."

PDP da Labour Party za su fafata da APC Uzodinma a Imo

Hakan dai na zuwa ne kwanaki uku gabanin zaɓen gwamnan jihar, inda a kwanakin baya wasu ƴan daba suka lakaɗawa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) duka a lokacin da ma’aikata ke zanga-zanga.

Masana harkokin siyasa sun ce za a fafata a zaɓen tsakanin ƴan takarar jam’iyyar PDP da Labour Party da kuma jam'iyyar APC mai mulki.

Gwamna Hope Uzodinma na jam’iyyar APC na neman yin tazarce, inda Samuel Anyanwu da Athan Achonu na PDP da Labour Party suka sha alwashin ƙwace kujerar gwamnan.

Makomar Uzodinma a Zaɓen Gwamnan Imo

A wani labarin kuma, an yi hasashen makomar gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a zaɓen gwamnan jihar na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Wani mai fashin baƙi kan al'amuran siyasa, Chizorom Ofoegbo, da aka fi sani da 'Ijele Speaks', yayi hasashen cewa Gwamna Uzodinma zai yi nasara a zaɓen

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng