Guguwar Sauya Sheƙa Ta Mamaye PDP, Mataimakin Shugaban Majalisa da Jiga-Jigai Sun Yi Murabus
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta ƙara rasa manyan jiga-jigai da ƙusoshinta waɗanda suka tabbatar da ficewa daga jam'iyyar
- Tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Odefa Obasi Odefa na cikin waɗan da suka miƙa takardar barin PDP
- Ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan zurafafa neman shawari daga iyalansa da kuma abokansa na siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) reshen jihar Ebonyi na ci gaba da rasa manyan jiga-jiganta a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
The Nation ta tattaro cewa a wannan karon, tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Odefa Obasi Odefa, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Mista Odefa tare da wasu kusoshi da masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP sun tabbatar da yin murabus daga kasancewa mambobin jam'iyyar a mazaɓar Onicha ta Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Odefa ya miƙa takardar ficewarsa ga shugaban PDP na gundumar Ogudu Okwor a ƙaramar hukumar Onicha ta Gabas, kamar yadda This Day ta ruwaito.
A ranar Laraba, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin ya tabbatar da haka ga manema labarai a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Jiga-jigan da suka bi sawunsa suka bar PDP
Ya ja ragamar jiga-jigan jam'iyyar PDP da Labour Party a ƙaramar hukumar, waɗan da duk suka sanar da ɗaukar matakin fice wa daga jam'iyyunsu.
Daga cikin jiga-jigan da suka mara masa baya wajen sauya sheƙa sun haɗa da shugabannin PDP na gundumomin Ugwu Oshiri, Okpuzor/ Ukawu, Ebyia Oshiri, Abaomege da dai sauransu.
Wani sashin takardar Odefa ya ce:
"Bayan tattaunawa da iyalina da abokaina, na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). Duba da haka, ina da yaƙinin cewa na yi iya bakin kokarina a PDP."
"Ina kuma miƙa godiya ga PDP bisa damar da na samu na yi wa al'umma hidima a lokacin da nake cikinta, ina muku fatan alheri kuma na gode."
Kotu ta tsige ƴan majalisa 3
A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin korar ƴan majalisun tarayya na PDP uku daga majalisar wakilan tarayya.
Yayin yanke hukunci ranar Talata, Kotun mai zama a Abuja ta ce PDP ta saɓa umarnin Kotu, don haka duk ƙuri'un da ta samu basu da amfani.
Asali: Legit.ng