Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Ministan Tinubu Wanda Ya Lashe Zaben Sanata a Jihar Arewa
- Kotun daukaka ta raba gardama a zaben Majalisar Tarayya a jihar Plateau tsakanin PDP da APC
- Kotun ta tabbatar da Ministan Ayyuka, Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben Plateau ta Kudu
- Kotun har ila yau, ta yi fatali da karar Napoleon Bali na jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar a watan Faburairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar Tarayya a jihar Plateau.
Kotun ta tabbatar da Ministan Ayyuka, Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben Plateau ta Kudu, Legit ta tattaro.
Wane hukunci kotun ta yanke a jihar Plateau?
INEC ta bi Umarnin kotun ɗaukaka ƙara, ta yi gyara a jerin sunayen 'yan takarar Gwamnan jihar Bayelsa
Kotun ta yi hukuncin ne a yau Talata 7 ga watan Nuwamba a Abuja bayan Lalong ya kalubalanci sakamakon zaben da aka gudanar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a mantaba a watan Faburairu ne hukumar zabe ta ayyana Napoleon Bali na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Yayin da ta ke bayyana sakamakon zaben, hukumar INEC ta ce Napoleon Bali na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 148,844, cewar Vanguard.
Wane sakamako INEC ta fitar a zaben Plateau?
Har ila yau, hukumar ta INEC ta bayyana cewa Simon Lalong na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 91,674 a zaben da aka gudanar a watan Faburairu.
Lalong ya bukaci kotun sauraran korafin zabe da ta rusa wannan hukunci na hukumar zabe yayin da kotun ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Bali na jam'iyyar PDP ya daukaka kara inda ta sake tabbatar da Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben na sanata mai wakiltar Plateau ta Kudu.
Kotun zabe ta tabbatar da Kingibe sanatar Abuja
A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da Ireti Kingibe ta jam'iyyar LP a matsayin wanda ta lashe zaben sanata mai wakiltar Abuja.
Kotun ta yi fatali da karar Philip Aduda na jam'iyyar PDP saboda rashin gamsassun hujjoji.
Sanata Adudu dai ya shafe shekaru da dama ya na kan kujerar sanatan birnin Tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng