Ga Mari, Ga Tsinka Jaka: APC Ta Yi Wa Peter Obi Raddi a Kan Batun Shari’ar Zaben 2023

Ga Mari, Ga Tsinka Jaka: APC Ta Yi Wa Peter Obi Raddi a Kan Batun Shari’ar Zaben 2023

  • Jam’iyyar APC ta maidawa Peter Obi martani a kan jawabin da ya gabatar game da rashin nasararsa a kotun karar zabe
  • Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka ya zargi ‘dan takaran LP a 2023 da nuna Gadara duk da bai lashe zabe ba
  • A cewar Morka, baya ga rashin nasarar LP a filin daga, ‘dan takaran hamayyar bai iya gamsar da kotu cewa an yi magudi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zargi Peter Obi na LP da kokarin nuna samun shugabancin kasar nan tamkar gadonsa ne.

APC ta yi martani ga ‘dan takaran shugaban kasar na LP a zaben 2023 bayan taron manema labarai da ya kira, Tribune ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani ga babatun Obi kan kotun koli, ya fadi dalilin da ya sa aka ki shi a zabe

Mr. Peter Obi ya yi Allah-wadai da hukuncin da kotun koli ta yi a kan shari’ar zaben shugaban kasa inda aka sake ba Bola Tinubu nasara.

Peter Obi
Peter Obi bai yarda da hukuncin zaben 2023 ba Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani jawabi da Felix Morka ya fitar ranar Litinin cikin dare, ya fadawa ‘dan adawan cewa da hujjoji ake yin nasara a kotu ba da ra’ayi ba.

Obi: Jawabin APC ta ofishin Felix Morka

"A taron ‘yan jarida da ya kira a yau (6 ga Nuwamba, 2023), Obi ya sake zargin hukumominmu, musamman kotu a kan rashin ba shi nasara
Ba saboda ya lashe zabe ba, ba saboda ya gamsar da kotu da hujjoji kamar yadda doka ta bukata ba, sai domin saboda shi ne Peter Obi."

- Felix Morka

Rahoton ya ce Sakataren yada labaran na APC ya zargi Obi da gadarar jin ya dace da mulki.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ban halarci zaman yanke shari’a a Kotun Koli ba, Peter Obi ya yi martani

Jam'iyyar APC ta fadi matsalar Peter Obi

Morka ya na ganin babbar matsalar da ‘dan takaran na LP ya samu a kakar siyasar bana ita ce rashin bambanci ra’ayinsa da kuma zahirin lamari.

A matsayin wanda ya ci ribar hukuncin kotun koli a shari’o’in zabe a baya, caccakar da Obi yake yi wa shari’a ya fito da girman kai da bakin cikinsa ne.

"Lokacin da kotu ta ba shi nasara, sai ya ce sun zama tubalin damukaradiyya, yanzu da bai dace ba, sai ya ce kotu sun ci amanar tsarin damukaradiyya."

- Felix Morka

Jawabin ya yi maraba da adawar da Obi ya shirya yi wa gwamnatin Bola Tinubu a mulki.

Bola Tinubu ya wanke kan shi

An samu labari jirgin shugaban kasa da aka gani a kasafin kudi jirgin sojojin ruwa ne, ba na Aso Rock Villa ba kamar yadda mutane su ka tunani.

Kara karanta wannan

Kotu ta shiga tsakani, ta yanke hukunci kan yunkurin tsige gwamnan PDP

Ana kiran wannan jirgi da jirgin shugaban kasa ne saboda irin manyan matakan tsaro da ya kunsa kuma tsohuwar gwamnati ta bukaci sayo shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng