Gwamna Ya Shiga Babbar Matsala, Masu Ruwa da Tsakin PDP Sun Goyi Bayan Ministan Tinubu
- Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP sun tabbatar da goyon bayansu ga Ministan Abuja, Nyesom Wike a rikicin jihar Ribas
- A wata sanarwa da suka rattaɓawa hannu, jagororin sun kuma yi Allah wadai da harin dabbanci da wasu suka kai majalisar dokoki
- A cewarsu, suna fatan kowane ɓangare zai rungumi hanyar zaman lafiya domin kawo karshen rikicin cikin lumana
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Manyan masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas sun ayyana goyon bayansu 100 bisa 100 ga Nyesom Wike.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa suna goyon bayan Wike, Ministan birnin tarayya Abuja dangane da rikicin siyasar da ya ɓarke a Ribas kwanan nan, The Nation ta ruwaito.
Bayan haka jagororin PDP daga gundumomin Ikwerre baki ɗaya sun amince da duk wata shawara da majalisar dokokkn jihar Ribas karkashin jagorancin, Martins Amaewhule, ta yanke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jiga-jigan PDP daga Ikwerre, ƙaramar hukumar da Wike da fito, sun bayyana matsayarsu ne a wata sanarwa da suka fitar bayan taron da suka yi ranar Litinin.
Shugabannin jam'iyyar PDP sun kuma yi tir da Allah wadai da harin bam ɗin da aka kai zauren majalisar dokokin jihar Ribas a makon da ya shige, rahoton Vanguard.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jagororin jam’iyyar PDP sama da 28, ta bayyana yunƙurin canza salon rikicin zuwa na ƙabilanci a matsayin abin da bai dace ba.
Masu ruwa da tsaki sun yi Allah wadai
Sun kuma ayyana karerayi da zarge-zargen da aka jefa wa Wike ciki harda ikirarin ya nemi kaso 25 na kudin shigar jihar Ribas a matsayin abun dariya.
Sanarwan ta ce:
"Muna nan daram tare da Jagoranmu wanda ba ya gajiyawa, Cif Nyesom Wike, tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma a yanzu mai girma Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT)."
“Mun yi tir da kakkausar murya kan harin dabbanci na matsorata da aka kai a zauren majalisar dokokin jihar Ribas a ranar 30 ga Oktoba, 2023."
"Saboda haka muna kira ga dukkan bangarorin da su rungumi zaman lafiya domin amfanin al’ummar jihar. Muna da tabbacin cewa halin da ake ciki yanzu zai ƙare da kyau."
Kamfanin wutar Kaduna ya kori ma'aikata
A wani rahoton na daban Kamfanin wutar lantarki na Kaduna ya kori ma'aikatansa akalla 39 daga aiki bisa zargin aikata laifuka daban daban.
A wata sanarwa da kakakin kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ya fitar.ya bayyana wasu daga cikin laifun da suka ja aka sallame su.
Asali: Legit.ng