Peter Obi Ya Caccaki Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Nasarar Tinubu, Ya Faɗi Illar da Ta Yi Wa Yan Najeriya

Peter Obi Ya Caccaki Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Nasarar Tinubu, Ya Faɗi Illar da Ta Yi Wa Yan Najeriya

  • Mista Peter Obi ya caccaki hukuncin Kotun ƙoli yana mai cewa ta rusa tunanin ƴan Najeriya na samun adalci a ɓangaren shari'a
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP ya faɗi haka ne yayin hira da ƴan jarida a Abuja ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023
  • Ya kuma godewa baki ɗaya al'ummar Najeriya bisa goyon bayan da suka bai wa LP a zaɓen da ya gabata

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, ya caccaki hukkuncin da Kotun ƙolin Najeriya ta yanke na tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Peter Obi yana jawabi ga yan jarida.
Peter Obi Ya Caccaki Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Nasarar Tinubu, Ya Faɗi Illar da Ta Yi Wa Yan Najeriya Hoto: Mr Peter Obi
Asali: Facebook

Mista Obi ya ce hukuncin ya tarwatsa ƙwarin guiwar da ƴan Najeriya ke da shi a ɓangaren shari'a na cewa zata kwato masu haƙƙinsu, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan hukuncin kotun koli

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi wannan furucin ne a Abuja ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023 a wurin taron manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta gaza a zaɓen 2023 - Obi

Ya kuma bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta nuna gazawa da rashin kwarewa a lokacin zaben da ya gabata a watan Fabrairu.

Idan baku manta ba a ranar 26 ga watan Oktoba, 2023, Ƙotun ƙoli ta kori karar Obi da Atiku Abubakar na PDP waɗanda suka kalubalanci nasarar shugaban Tinubu.

"Demokuraɗiyyar mu ce ta fi cutuwa da wannan wasan kwaikwayon da aka yi a Kotu. Babu tantama, hukuncin ya haddasa tangarɗa a yarda da ƙwarin guiwar da mutane ke da su a fannin shari'a.
"A matsayin ƴan takarar jam'iyyar mu, ni da Datti, mun gama amfani da damar da kundin tsarin mulki ya bamu. Sai dai wannan ƙarshen mafari ne a burin mu na gina sabuwar Najeriya."

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Luguden wutar sojojin Najeriya ya halaka ƴan ta'adda sama da 160 a jihohin arewa 2

"Wannan shekara ta 2023 ta zo da abubuwan ban mamaki, INEC ta gaza sauke nauyin da doka ta ɗora mata, ta nuna rashin iya aiki."

- Peter Obi.

Daga ƙarshe, Peter Obi ya miƙa godiyarsa ga ƴan Najeriya bisa nuna goyon bayan LP a babban zaben 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu aka fara - Peter Obi

A wani rahoton kuma Peter Obi ya ce rashin nasarar da ya samu a Kotun koli ba tana nufin burinsa na gina sabuwar Najeriya ya zo ƙarshe ba.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce tun da an kawo ƙarshen shari’a, yanzu jam’iyyar Labour Party tana ɓangaren adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262