Bidiyon Wani Dan Siyasa a Arewa Ya Sha Kunya Yayin Kaddamar da Rijiyar Burtsatse, Babu Ruwa

Bidiyon Wani Dan Siyasa a Arewa Ya Sha Kunya Yayin Kaddamar da Rijiyar Burtsatse, Babu Ruwa

  • Jigon jam’iyyar PDP, Dele Momodu ya wallafa wani faifan bidiyo inda wani dan siyasa ya sha kunya yayin kaddamar da rijiyar burtsatse
  • A cikin faifan bidiyon, an gano wani dan siyasa ya na kaddamar da rijiyar burtsatsen amma ta ki kawo ruwa lokacin da ya murda ta
  • Faifan bidiyon ya jawo martanin jama’a da dama inda mafi yawanci su ka soki dan siyasar da gazawa a kokarin burge mutanen yankinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba – An gano wani dan siyasa da ba a bayyana ko waye ne ba a cikin takaici a wani faifan bidiyo na kokarin burge ‘yan yankinsa, Legit ta tattaro.

A cikin faifan bidiyon, an gano dan siyasar na kaddamar da rijiyar burtsatse a yankinsa, amma abin mamaki ta ki kawo ruwa lokacin da ya ke kokarin wainata.

Kara karanta wannan

“Kasuwa ta yi kyau”: Mabaraciya ta siya soyayyar kaza, ta darje ta zabi wanda take so

Bidiyon dan siyasa na takaici bayan shan kunya yayin kaddamar da rijiyar burtsatse
Bidiyon dan siyasar yayin da ya ke murda rijiyar burtsatse. Hoto: @delemomoduovation.
Asali: Instagram

Waye ya wallafa faifan bidiyon?

Jigon jam’iyyar PDP, Cif Dele Momodu shi ya wallafa faifan bidiyon na abin kunya a shafinsa na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano dan siyasar na ta waina rijiyar burtsatsen don ta kawo ruwa amma har ya gaji babu abin da ya fito daga rijiyar.

Har ila yau, ‘yan kauyen da ke tsaye a wurin bikin kaddamarwar sun yi cirko-cirko don ganin ruwa ya kawo amma shiru ba abin da ya fito.

Mene Dele Momodu ya ce kan bidiyon?

Momodu ya yi rubutu yayin wallafa faifan bidiyon kamar haka:

“Yayin kaddamar da aiki a jihar Taraba, lokacin da Injiniya ya ke son ba ka kunya, abin da rikitarwa, ni ba neman fada na ke yi ba, kawai na wallafa ne don raha.”

Mutane dama sun yi martani kan wannan faifan bidiyo na Momodu:

Kara karanta wannan

So gamon jini: Daga yanke mata farce, kyakkyawar budurwa ta fada soyayya da mai yankan kumba

@levisimeon:

“Shirme, meyasa bai kaddamar da aikin da ‘Solar’ ba saboda mutane su samu saukin sarrafa shi, abin dariya.”

@frank_anani_lebon:

“Ruwa na fitowa daga sama, ka ci gaba da wainaya.”

Lauya ya bai wa Atiku, Obi shawara kan hukuncin kotun koli

A wani labarin, shahararren lauya ya bai wa Atiku Abubakar da Peter Obi shawara kan abin da da za su yi bayan hukuncin kotun koli.

Lauyan mai suna Inibehe Effiong ya ce ya kamata Majalisar Tarayya ta sake fasali a dokar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.