Zaben Kogi: Kungiya Ta Nemi a Kama Dino Melaye Kan Dalili 1 Tak, Ta Yi Bayani
- Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta yi kira ga jami’an tsaro da su cafke dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Kogi
- Kungiyar na zargin Melaye da aikata ta’addanci yayin zaben Majalisar Tarayya da aka gudanar a 2007
- Ta kuma bukaci sifetan ‘yan sanda, Kayode Egbetokun da ya yi gaggawar kame wadanda su ke da hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi – Gamayyar Kungiyoyin Kare Muradun Al’umma ta bukaci a kama dan takarar gwamna a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne kan zargin ta’asar da Melaye na jam’iyyar PDP ya aikata a shekakar 2007, Legit ta tattaro.
Mene kungiyar ke cewa kan Dino Melaye?
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a makon da ya gabata, shugabanta, Wisdom Chinedu ya bukaci sifetan ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya kamo Melaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar na zargin Melaye da PDP da zargin ta’addanci kan abokan hamayyarsa a zaben da ya yi nasara a mazabar Kabba/Bunu/Ijumu a shekakar 2007.
Daga cikin wadanda su ka rasa ransu akwai Mista Jimoh Asimi da Honarabul Victor Obafaiye yayin rikicin, cewar Leadership.
Mene ya faru a Kogi a 2007?
Mista Asimi shi ne wakilin jam’iyyar ACN kafin ta hade da sauran jam’iyyu su dawo APC, sai kuma Obafaiye shi ne shaida a shari’ar zaben da aka gurfanar da Melaye.
Dan takarar jam’iyyar a zaben, Honarabul Richard Akanmode ya gurfanar da Melaye a gaban kotun zaben kan magudi da ta’addanci.
Sanarwar ta ce:
“Yayin da ake shari’ar zaben, Honarabul Akanmode ya na da wani shaida wanda a idonsa komai ya faru inda mutane da dama su ka tsira da kyar.
“Abin takaici, ana saura kwana daya a koma kotu, Obafaiye ya samu kirar waya a daren ranar Lahadi inda aka umartce shi da ya fito waje.
“Wannan ita ce ranar ta karshe da sake jin duriyar Obafaiye inda aka fasa masa kayi a wannan ranar.”
Fasto ya yi hasashen zaben Kogi
A wani labarin, wani Fasto ya yi hasashen wanda zai yi nasara a zaben jihar Kogi a watan Nuwamba.
Fasto Godwin Ikuru shi ya bayyana haka inda ya ce Usman Ododo na jam'iyyar PAC shi zai lashe zabe.
Asali: Legit.ng