Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Zaben Jihar Arewa Wanda Bai Kammala Ba, Ta Ba da Sabon Umarni
- Kotun daukaka ta yi hukunci kan shari'ar zaben dan Majalisar Tarayya a jihar Katsina
- Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun zabe da ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba
- Tun farko, hukumar zabe ta INEC ta ayyana Jamilu Mohammed na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Jamilu Mohammed na jam'iyyar PDP kan hukuncin kotun zabe a jihar Katsina.
Kotun zaben dai ta bayyana zaben Majalisar Tarayya a mazabar Faskari/Kankara/Sabuwa a matsayin wanda bai Kammala ba, Legit ta tattaro.
Wane hukunci kotun ta yanke kan zaben Katsina?
Har ila yau, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kotun zaben da ke zamanta a Katsina ta umarci hukumar INEC da sake zabe a wasu mazabun kananan hukumomin Faskari da Kankara.
Mai Shari'a, Moore Aseimi shi ya yanke wannan hukunci a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba, cewar The Nation.
Wane umarni kotun ta bai wa mai kara a Katsina?
Yayin hukuncin, Aseimo ya tabbatar da hukuncin kotun zaben da ta ce bai kammala ba inda ya ci taran Mohammed Naira dubu 300.
Ya umarci Mohammed ya biya dan takarar jam'iyyar APC, Shehu Dalhatu Tafoki kudaden da aka ci tararshi.
Tafoki shi ne tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar da ya sauka a 'yan kwanakin nan.
Kotun ta umarci sake zaben a mazabu 20 cikin kwanaki 30 kacal bayan yanke hukuncin kotun.
Kotun daukaka kara ta rusa zaben sanatan Abia
A wani labarin, kotun daukaka kara ta rusa zaben Sanata Darlington Nwokocha na jam'iyyar LP a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba.
Kotun, har ila yau, ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, Kanal Austin a matsayin wanda ya lashe zaben.
Wannan hukunci ya tabbatar da sanatoci biyu kenan 'yan jam'iyyar PDP da ke wakiltar Kudu maso Gabas a majalisar.
Asali: Legit.ng