Shehu Sani Ya Shawarci Gwamna Fubara Kan Yadda Zai Yi Maganin Wike
- Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi tsokaci kan rikicin siyasar da ya ɓarke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ubangidansa a siyasance, Nyesom Wike
- Rikicin ya taso ne a daidai lokacin da ƴan majalisar da ke biyayya ga Wike suka yi yunkurin tsige Gwamna Fubara, inda suka zarge shi da ƙoƙarin karɓe tsarin siyasar jihar daga hannun Wike
- Sani ya shawarci Gwamna Fubara da ko dai ya faranta wa Wike rai ko kuma ya ƙalubancesa ya yi nasara a kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, ya yi tsokaci kan rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ubangidansa a siyasance, Nyesom Wike.
An zargi gwamnan Rivers da ƙoƙarin ƙwace tsarin siyasar jihar daga hannun magabacinsa, Wike, wanda ya taimaka masa ya hau mulki.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, da wasu dattawan siyasa a jihar Kudu maso Kudu sun shiga tsakani domin kawar da rikicin siyasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da haka, Wike ya dage cewa ba zai naɗe hannunsa ba ya bari a ƙwace masa tsarin siyasar jihar Rivers ba.
Wike: Shehu Sani ya baiwa Fubara shawara
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), Sanata Sani, jigo a jam'iyyar PDP, ya ce Gwamna Fubara, dole ya zaɓi matsaya kan rikicin siyasar da ke tsakaninsa da wanda ya gabace shi.
Sani ya ce gwamnan na jihar Rivers yana da zaɓi biyu, ko dai ya gamsar da Wike ko kuma ya yaƙe shi ya yi nasara.
Kalamansa:
"Zuwa ga Mista Sim;
"Idan ka yi abokantaka da Damisa, dole ne ka ciyar da ita da faranta mata rai, ko dole ka yi yaƙi sannan ka yi nasara a kan Damisar. Babu wani batun zama babu zaɓi kamar tsayawa yin addu'a da lallaɓa Damisar domin a samu zaman lafiya."
Gwamna Fubara Ya Nemi Afuwa
A wani labarin kuma, Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya nemi afuwar al'ummar jihar kan rikicin siyasar da ya ɓarke a jihar.
Ya bayyana rikicin a matsayin "Abin nadama da damuwa na 'yan kwanakin da suka gabata," yana mai cewa yana da mahimmanci a yi sadaukarwa don zaman lafiya ya ɗore.
Asali: Legit.ng