An Yi Ruwan Mari a Taron Masu Ruwa da Tsakin PDP a Taraba? Tsohon Dan Majalisa Ya Fasa Kwai

An Yi Ruwan Mari a Taron Masu Ruwa da Tsakin PDP a Taraba? Tsohon Dan Majalisa Ya Fasa Kwai

  • Takkadama ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP da aka yi a jihar Taraba
  • Rahotanni sun ce tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Hon. Douglas Ndatse, ya yi ruwan mare-mare a taron
  • Sai dai, Natse ya karyata zargin yana mai cewa magauta ne ke kokarin bata masa suna saboda dalili na son zuciyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Taraba kuma jigon PDP, Hon. Douglas Ndatse, ya karyata rade-radin da ke yawo cewa ya mari mutane a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Ndatse wanda ya wakilci mazabar Donga a majalisar dokokin jihar ya karyata hakan ne a ranar Juma'a, 3 ga watan Oktoba, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

Douglas Ndatse ya ce bai yi mare-mare ba
An Yi Ruwan Mari a Taron Masu Ruwa da Tsakin PDP a Taraba? Tsohon Dan Majalisa Ya Fasa Kwai Hoto: Punch
Asali: UGC

"Ban mari kowa ba ana so a bata mani suna ne", Ndatse

Ya bayyana cewa ikirarin da wani mai suna Garerie Suntai ya yi cewa ya mammari duk mutanen da ya ci karo da su a taron masu ruwa da tsakin na PDP, bai da tushe balle makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon siyasan ya yi zargin cewa wasu ne suka zauna suka kagi labarin domin bata masa suna, yana mai jaddada cewar bai mari kowa ba kuma shi baya adawa da tsarin karba-karba.

A cewarsa, jiga-jigan PDP a Donga sun zauna sannan suka yarda cewa ya kamata ciyaman ya fito daga kalibar Ikpan.

Ya ce:

"Hon. Istifanus Gbana wanda shine shugaban dattawan Ikpanzum bai tsayar da dan takarar hadin gwiwa ba, maimakon haka sai ya gabatarwa kwamiti da yan takara bakwai don gwamnan ya zabi mutum daya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

"Abun dariya ne ace ni ina adawa da tsarin karba-karba a lokacin da duk muka zauna kuma muka rarrabawa kabilu mukamai a karamar hukuma tare. A taron, an ba kabilar Ichen kujerar mataimakin ciyaman yayin da Tiv suka karbi sakatare.
"A wajen gabatar da rahoton ga kwamirin PDP, dattijo Kitsubimka ya lura da wani abu cewa wasu mutane da suka yi ikirarin su masu ruwa da tsaki a PDP ne ba mambobin jam'iyyar bane wanda hakan gaskiya ne, sai Mista Garerie da tawagarsa suka fara zagin dattawa harda ni sai muka taushi zuciyarmu.
“Gararie Suntai yaro ne da ni na rene da shi a siyasa kuma na yi mamaki cewa zai iya yi mani wannan karyan don cimma wasu ra'ayi nasa. Akwai manyan mutane a wannan taron, kuma ina mai kalubalantarsa da ya kira sunan wani babba da abun ya faru a kan idonsa baya ga shi idan yana son tabbatarwa duniya cewa ba daukar nauyinsa aka yi don ya bata mani suna ba."

Kara karanta wannan

Matar aure ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta bayan shekaru 2 babu haihuwa

Abun da ya faru a taron

Tsohon dan majalisar ya yi bayanin cewa shi dai kawai ya yi adawa ne da sunan dan takarar mataimakin shugaban jam'iyyar da aka sanar a wajen taron ba tare da saninsa ba da na sauran masu ruwa da tsaki a karamar hukumar.

Ya ci gaba da cewa:

"An mika kujerar mataimakin ciyaman zuwa Ichen (kabilata) sannan muka zauna muka ce, idan ciyaman ya fito daga Donga ta kudu za mu zabi mataimaki daga arewa haka kuma idan aka samu akasin haka.
"Amma ga mamakinmu, koda dai har yanzu ana fafatawa kan kujerar ciyaman din, wani ya rubuta sunan wani a matsayin mataimaki sabanin abun da muka yanke a matsayin mutanen Ichen.
"Mun tattauna a taron cewa za a yi tarurruka da dama ba tare da an sako shugabannin gudunma ko mukaddashin shugaban karamar hukumar ba. Don haka, kawai na fadi abun da ke zuciyana ne sannan mutane da dama suka yarda dani.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ta Maka Wani Mutum a Kotu Kan Bata Mata Suna

"A matsayina na dan jam'iyya, na jajirce wajen ganin PDP ta yi nasara kuma zan dunga yin magana a duk lokacin da aka yi ba daidai ba. Zargin cewa na mammari mutane a wajen taron ba shi da tushe balle makama, don haka ina kira ga tarin magoya bayana da jama’a da su yi watsi da shi."

Jiga-jigan PDP sun maka Tinubu a kotu

A wani labarin, mun kawo cewa Aniekan Akpan, shugaban PDP a jihar Akwa Ibom da sakataren jam'iyyar, Harrison Ekpo, sun maka Shugaban Kasa Bola Tinubu a kotu.

An kuma maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Obot Akpabio ma a kotun, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng