Bayan Kwace Nasarar APC, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Zaɓen Sanatan Kogi Ta Gabas

Bayan Kwace Nasarar APC, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Zaɓen Sanatan Kogi Ta Gabas

  • Kotun ɗaukaka kara ta raba gardama kan zaɓen Sanatan Kogi ta gabas wanda aka yi a watan Fabrairun, 2023
  • Da take yanke hukunci, Kotun ta soke hukuncin da Kotun zaɓe ta yanke, inda ta tabbatar da nasarar Sanata Isah na jam'iyyar APC
  • A baya Kotun sauraron kararrakin zaɓe ta kwace nasarar Sanatan, kuma ta umarci a canja zaɓe a wasu rumfuna 94

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da nasarar shugaban kwamitin kwastam na majalisar dattawa, Sanata Jibrin Isah.

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben Kogi ta gabas.
Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tabbatar da Jibrin Isah a Matsayin Sanatan Kogi Ta Gabas Hoto: channelstv
Asali: UGC

Yayin zaman yanke hukunci ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, Kotun ta bayyana cewa shaidun da Kotun zaɓe ta dogara da su ba su inganta ba.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar ɗan majalisar tarayya daga Kaduna

Sakamakon haka Kotun ɗaukaka karar ta yanke yin fatali da dukkan bayanan da shaidun suka yi a shari'ar sahihancin zaɓen Sanata Isah, mai wakiltar Kogi ta gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka kuma Kotun ta jingine hukuncin da Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yanke, sannan ta tabbatar wa Isah da kujerarsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Tun da farko dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Isah na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kogi ta Gabas.

INEC ta bayyana haka ne jim kaɗan bayan kammala tattara sakamkon kuri'un da aka kaɗa a zaben wanda aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Hukuncin da Kotun zaɓe ta yanke

Amma ɗan takarar Sanatan a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Victor Adoji, wanda ya zo na biyu, ya kalubalanci wannan sakamako a gaban Kotun zaɓe.

Kara karanta wannan

Ndume da Lawal: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sahihancin nasarar Sanatocin arewa 2

Ya shaida wa Alkali cewa ƙuri'un runfunan zaɓen da INEC ta soke sun zarce tazarar da ke tsakaninsa da wanda ya aka ce ya samu nasara, Daily Post ta ruwaito.

Bugu da ƙari, ya roƙi Kotun ta soke nasarar Isah kana ta bada umarnin shirya sabon zaɓe a akwatuna 94 da lamarin ya shafa a mazaɓar Sanatan Kogi ta gabas.

Kuma yayin da take yanke hukunci, Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben ta umarci INEC ta shirya zaɓe a rumfuna 94, inda aka samu matsala a zaɓen da ya wuce.

Sai dai bisa rashin gamsuwa da wannan hukunci, Sanata Isah ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun gaba, wanda a yanzu ta tabbatar masa da nasara.

Gwamnonin PDP sun kare kansu

A wani rahoton na daban Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bayyana dalilinsu na mara wa shugaban ƙasa Tinubu baya kan rikicin siyasar jihar Ribas.

A cewarsu, saɓanin tunanin masu sukar hakan wanda ke tare da Atiku, tsoma bakin Tinubu ya zama wajibi kuma dole a yaba masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262