Zaben Gwamnoni: Shugaba Tinubu Ya Mika Tutocin APC Ga Ododo, Uzodinma da Sylva, Bayanai Sun Fito

Zaben Gwamnoni: Shugaba Tinubu Ya Mika Tutocin APC Ga Ododo, Uzodinma da Sylva, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya miƙa tutar jam'iyyar APC ga ƴan takara uku na jam’iyyar gabanin zaɓen gwamnoni da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Kogi, Imo, da Bayelsa
  • Ƴan takarar da aka miƙa wa tutocin APC su ne Gwamna Hope Uzodimma na Imo, wanda ke neman wa’adi na biyu, Timipre Sylva na Bayelsa da Usman Ododo na jihar Kogi
  • Taron wanda ya gudana a cikin daƙin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban ƙasa, ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da sauran mambobin kwamitin NWC

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa tutocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ga ƴan takarar gwamna uku na jam’iyyar gabanin zaɓukan da za a yi a wannan watan a jihohin Kogi, Imo, da Bayelsa.

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya ta amince da ƙarin kasafin kuɗin da Tinubu ya tura na 2023, bayanai sun fito

Wadanda aka baiwa tutocin dai sune Gwamna Hope Uzodinma na Imo, wanda ya tsaya takara karo na biyu, Timipre Sylva na jihar Bayelsa da Usman Ododo na jihar Kogi, jaridar The Nation ta ruwaito.

Tinubu ya ba ƴan takarar APC tutoci
Shugaba Tinubu ya ba Ododo, Uzodinma da Sylva tutocin APC Hoto: Abdullaziz Mohammed
Asali: Facebook

Taron wanda ya gudana a cikin ɗakin taro na Banquet Hall na fadar shugaban ƙasa, ya samu halartar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar (NWC), da wasu baƙin ƴan takarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 11 ga watan Nuwamba ne dai za a gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Imo, Kogi, da Bayelsa.

Zaɓen 2023: Zaɓuɓɓukan da ba su a jadawalin babban zaɓe

Zaɓe ya sake kusantowa sai dai a wannan karon za a gudanar da su ne a wasu zaɓaɓɓun jihohin ƙasar nan.

Zaɓuɓɓukan da ba su a cikin jadawalin babban zaɓe ana gudanar da su ne daban.

Kara karanta wannan

"Yaran Tinubu ne": Atiku ya caccaki gwamnonin PDP bisa shiga tsakani a rikicin Wike, Fubara

Abin da yake sanya wa ana samun irin waɗannnan zaɓɓɓukan shi ne ƴan takara da yawa ba su gamsuwa da sakamakon zaɓe, sai su garzaya kotu domin neman haƙƙinsu.

A wasu lokutan kotunan zaɓe, suna soke nasarar da gwamnonin suka samu tare da bayar da umarnin a sake zaɓe, wanda hakan yake sanya wa su fita daga cikin jadawalin lokacin gudanar da babban zaɓe.

Fasto Ya Hango Wanda Zai Lashe Zaɓen Kogi

A wani labarin kuma, fasto Godwin Ikuru ya yi hasashen ɗan takarar da zai yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Faston ya bayyana cewa Ahmed Usman Ododo, ɗan takarar jam'iyyar APC ne zai yi nasara domin shi ne zaɓin Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng