Wike Ya Karyata Rade-Radi, Ya Shaidawa Gwamnonin PDP Silar Rigimarsa da Gwamnan Ribas
- Ministan harkokin birnin tarayya na Abuja ya yi karin haske a kan rikicinsa da Gwamna Simi Fubara a Ribas
- Nyesom Wike ya fadawa Gwamnonin PDP cewa abin da ya haddasa rigimar siyasar shi ne neman bata gininsa
- A cewar Ministan kasar, ba za ta yiwu Gwamnan Ribas ya jawo abokan fadansu bayan sun yi galaba a zabe ba
Abuja - Ministan harkokin birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike ya ce babu wanda ya isa ya ture ginin siyasar da ya kafa a jihar Ribas.
A lokacin da ya zanta da Gwamnonin jihohin PDP da su ka ziyarce shi a ofishinsa a ranar Talata, ya Nyesom Wike ya bude masu bakinsa.
Ministan Abujan ya ce ba za ta yiwu a gurganta karfin siyasarsa a gida ba, ya ce zai yaki duk wani wanda ya nemi ya yi masa rashin adalci.
Vanguard ta ce Wike ya fadawa gwamnonin cewa babu wani da ya isa ya yi masa barazana, ya na magane a
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike: Dalilin rikicin jihar Ribas
"Sun yi magana a kan rikicin siyasar jihar Ribas. Bari in fadawa duk wanda yake bukatar sauraro, babu wanda ya isa ya yi mani barazana.
Babu bambanci ko a kawo ‘yan iska ko ka ce kai Ijaw ne. Idan zan yi abu, zan yi. Tsige mai mulki ba juyin mulki ba ne, akwai shi a doka.
- Nyesom Wike
Kudi Wike ya ke nema a Ribas?
"Game da jita-jitar kudi da sauransu, duk shirme ne. Yaushe na bar ofis? Kuma ina Ministan Abuja
Amma babu wanda zai iya rusa ginin siyasarmu, babu wanda ya isa. Ba za mu yi aiki, sai ka dauka makiya; wadanda su ka yake ba, ba a haka.
- Nyesom Wike
Daily Trust ta ce Ministan ya musanya zargin neman 25% na dukiyar Ribas, ya ce shi ba maras godiya ba ne, rigimarsu ta siyasa ce kurum.
Babu maganar APC ko PDP ga Wike
A nan ma Wike ya nanata abin da ya saba fada na cewa babu ruwansa da PDP ko APC, tsohon Gwamnan ya ce kishin kasa ya kawo shi ofis.
Bari in gode maku ‘yanuwa da abokai na a kan wannan ziyara mai ban sha’awa, domin godewa shugaban kasa da ya ba ni mukamin nan.
Na fadawa kowa karara cewa ba wata jam’iyya na zo yi wa aiki a nan ba. Na zo ne saboda kishin Najeriya da zaman lafiya, ni ‘Dan PDP ne.
Asali: Legit.ng