Magana Ta Fito: Manyan Abubuwa 2 da Suka Haddasa Rigima Tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Magana Ta Fito: Manyan Abubuwa 2 da Suka Haddasa Rigima Tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Rahotanni sun kawo cewa alaka ta yi tsami tsakanin Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Ribas da magajinsa, Gwamna Siminalayi Fubara, a jihar.

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun

Kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto, rigima ya kaure tsakanin Gwamna Fubara da ubangidansa a siyasa, Wike saboda wasu matakai da gwamnan na PDP ya dauka a jihar Ribas.

Alaka ta yi tsami tsakanin Wike da Fubara
Abubuwa 2 Da Suka Rura Wutan Rikici Tsakanin Wike Da Gwamna Fubara Na Ribas Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

An tattaro cewa majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige gwamnan kasa da awanni 12 bayan wasu yan daba da ba'a san ko su wanene ba sun kona ginin majalisar.

Wike, Amaechi, Fubara: Abubuwan da ya kamata a sani game da rikicin siyasar Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa a kan yunkurin tsige Gwamnan jihar Ribas

Da farko majalisar ta dakatar da shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Ehie Edison, kafin aka fara shiri kan gwamnan.

Yan majalisa 24 cikin 32 sun sanya hannu a tsarin tsige gwamnan.

Ga dalilai biyu da suka sa ake shirin tsige gwamnan a kasa:

1. Nada sabbin kwamishinoni ba tare da izinin Wike ba

Da farko Fubara ya rantsar da kwamishinoni 14 da ayyukansu a majalisarsa amma bayan shan suka daga bangarorin adawa, sai gwamnan ya rantsar da wasu karin kwamishinoni biyar wadanda majalisar ta tantance tare da tabbatar da su.

Rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara da magabacinsa Wike ya fito fili bayan rantsar da kwamishinonin.

2. Farfado da aikin Amaechi

An kuma tattaro cewa Gwamna Fubara ya yi yunkurin farfado da gonar Shonghai da sauran tsare-tsaren da ake sa ran zai amfani mutanen jihar.

Sai dai kuma, Gonar Shonghai aiki ne da tsohon gwamna Rotimi Amaechi, wanda ya rike mukamin ministan sufuri a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya fara.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamna ya sa labule da manyan dattawan PDP da Sarakunan jiharsa, bayanai sun fito

Amaechi ya kasance babban abokin hamayyar Wike a siyasar jihar kuma ana ganin cewa ba'a yi tsammanin Gwamna Fubara zai yi wannan yunkuri da zai sa ayi zargin yana shirin sauya sansani ba.

Ribas: Gwamnonin PDP sun kira taron gaggawa

A wani labarin, mun ji cewa a sakamakon abubuwan da ke faruwa a jihar Ribas, gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP sun kira taro.

A rahoton da Tribune ta fitar, an fahimci cewa kungiyar gwamnonin PDP watau PDP-GF za ta yi wannan zama na musamman ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng