Dattijon Neja Delta Ya Fadi Wanda Wike Yake So Ya Kakaba Ya Zama Gwamnan Ribas
- Edwin Clark ya fito ya ba Gwamnan jihar Ribas, Simi Fubara kariya daga ‘shirin’ da Nyesom Wike yake yi masa
- Tsohon Ministan sadarwan ya zargi tsohon Gwamna da kokarin juya magajinsa, abin da shi kuma bai dauka ba
- A wani jawabinsa, Cif Clark ya ce ana harin maida Martins Amaehwule ya zama Gwamna idan an tsige Fubara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Delta - A matsayinsa na dattijo kuma shugaban kungiyar PANDEF, Edwin Clark ya zargi Nyesom Wike da yunkurin ganin bayan Sim Fubara.
Daily Trust ta rahoto Cif Edwin Clark ya na cewa akwai hannun Ministan harkokin birnin Abuja a rikicin siyasar da ake neman jefa jihar Ribas.
A cewar Clark, burin Nyesom Wike shi ne majalisar dokoki ta tunbuke Gwamna Simi Fubara.
Za ayi waje da Gwamna da mataimakiyarsa a Ribas
Da an yi waje da Mai girma Gwamnan, Cif Clark ya ce Wike zai tursasawa Farfesa Ngozi Nma Odu ta yi murabus daga mataimakiyar gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan Farfesar ta sauka daga kujerarta, wanda yake kan layi a tsarin mulki shi ne shugaban majalisar dokokin da yanzu ya ke tare da su Wike.
Ribas: Fubara ya taya Edison Ehie murna
Saboda Hon. Edison Ehie ya hana a tsige Gwamna Fubara ne ya rasa mukaminsa na shugaban masu rinjaye, ‘yan majalisa su ka tunbuke shi yau.
Jim kadan da yin haka aka ji Gwamnan Ribas ya na taya Edison Ehie murnar zama sabon shugaban majalisar dokoki, hakan ya sake jawo rudani.
A rahoton the Cable, Clark ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gargadi tsohon gwamna watau Wike da jami’an tsaron Ribas.
Dattijon ya ce ana so a sake kakaba mutumin Ikwere a mulki, don haka dole Tinubu ya hanzarta ya dauki mataki domin hana rikicin ya yi kamari.
Shawarar Clark ga Tinubu
"Bari in ja-kunne da kyau, ba za mu bari hakan ta faru a. Dole shugaban kasa Bola Tinubu ya gargadi Nyesom Wike da jami’an tsaron Ribas.
Abin da zai biyo baya ba zai yi wa yankin da kuma tattalin arzikin kasa kyau ba. Laifin menene Fubara ya yi? Saboda ya ki bari a rika juya shi.”
- Edwin Clark
Ana da labari Hon. Edison Ehie wanda ‘dan gani-kashenin Simi Fabura ne da yake ba shi kariya a Majalisa ya rasa kujerar da yake kai a Ribas.
Alamu na nuna akwai sabani tsakanin Gwamnan Ribas da ubangidansa a siyasa, Nyesom Wike, wanda ya samu sabani da Rotimi Amaechi.
Asali: Legit.ng