Maganar Tsige Gwamnan Ribas Ta Yi Nisa, An Yi Waje da Masoyinsa Daga Kujerar Majalisa
- Dambarwar siyasar jihar Ribas ta yi sanadiyyar da Edison Ehie ya rasa kujerar da yake kai a majalisar dokoki
- A yau aka yi wani zaman samammko, ‘yan majalisar Ribas su ka amince a tsige shugaban marasa rinjaye a jihar
- Masu adawa da Simi Fubara su na yi wa Honarabul Ehie kallon ala-ka-kai wajen fatattakar Gwamna daga ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Rivers - Rikicin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas ya dauki wani fasali na dabam yayin da aka shigo wani sabo mako a yau dinnan.
A safiyar Litinin, labari ya fito daga Daily Trust cewa an tsige Edison Ehie daga matsayinsa na shugaban masu rinjaye a majalisa.
Hon. Ehie wanda ya na cikin manyan magoya bayan Similanayi Fubara ya rasa matsayinsa ne a sakamakon rikicin siyasar Ribas.
Ana so a tsige Gwamnan Ribas a Majalisa?
Ana zargin ‘dan majalisar na Ahoada ta Gabas II ya kawo tasgaro da aka nemi a fara yunkurin tunbuke Gwamna Fubara a kan mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun ana yi kamar wasa, yanzu rade-radin kokarin tsige Mai girma Gwamnan jihar Ribas ta yi karfi, har ta kai ya fito ya na magana.
Shugaban majalisar dokokin Ribas, Rt. Hon. Martins Amaehwule ya ce an sauke Ehie daga matsayinsa ne saboda bai zuwa majalisa.
'Yan majalisa 17 sun tunbuke Edison Ehie
Amaehwule ya ce ‘yan majalisa 17 sun goyi bayan matakin da aka dauka a yau a daidai lokacin da magoya baya su ke zanga-zanga.
Jaridar Leadership ta ce tun karfe 7:00 na safiyar yau ‘yan majalisar su ka yi sammako, su ka zauna domin yanke hukuncin nan.
Wanene Hon. Edison Ehie?
‘Yan majalisa 23 su ke zauren majalisar dokokin a zaman da aka yi, da alama an samu wasu ‘yan tsirarru da ke tare da Edison Ehie.
Tun 2015 Ehie ya zama ‘dan majalisa, bayan nan ya lashe zabe sau biyu a jere a Ahoada.
Kafin zuwansa majalisa, shi ne shugaban matasan PDP na karamar hukumar Ahoada ta gabas, baya ga siyasa, ya kan taba kasuwanci.
Za a tsige Gwamna ko kuwa zai sha?
Ana jita-jita cewa 'yan majalisar dokokin Jiha za su tsige Mai girma Gwamnan Ribas watanni biyar da karbar mulki a hannun Nyesom Wike.
A sakamakon gobarar da ta barke, jami’an tsaro sun zagaye harabar Majalisar dokokin Ribas, yayin da magoya baya su ke ta zanga-zanga.
Asali: Legit.ng