Peter Obi Ya Shiga Yar Buya Bayan Ya Sha Kaye a Kotun Koli? Kakakin Kamfen Din LP Tanko Ya Magantu
- Ana ta rade-radin cewa dan takarar shugaban kasa na jama'iyyar LP, Peter Obi, ya shiga yar buya bayan kotun koli ta tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu
- Sai dai kuma, kungiyar kamfen dinsa ta fayyace cewa ya tafi kasar waje kafin sanar da ranar yanke hukuncin
- Kotun kolin ta yi watsi da karar da Obi da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP suka shigar, inda ta tabbatar da nasarar Tinubu
FCT, Abuja - Kungiyar kamfen din jam'iyyar LP ta yi martani kan rade-radin cewa dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, ya shiga yar buya bayan hukuncin kotun koli da ta tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Legit Hausa ta rahoto cewa babbar kotun ta yi fatali da kararrakin da Obi da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar suka shigar a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.
Kwamitin kotun mai mutum bakwai ya tabbatar da nasarar Tinubu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Hukuncin kotun koli: Peter Obi ya yi gum
Biyo bayan hukuncin kotun kolin, yan Najeriya da dama sun yi tsammanin Obi zai yi jawabi don bayyana matsayinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi gum da baki, bai ce uffan ba har yanzu, lamarin da ya haddasa jita-jitan cewa ya shiga yar buya ko kuma yana jin ciwon kayen da ya sha.
Ana haka, kakakin kungiyar yakin neman aben Obi-Datti, Yunusa Tanko, ya yi watsi da rade-radin, rahoton Punch.
Tanko ya ce Obi ya fita wajen kasar tun kafin takardar yanke hukuncin kotun koli ta iso.
Malamin addini ya magantu kan zaben 2027
A wani labarin, fitaccen malamin addini, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi watsi da damar Peter Obi na zama shugaban kasa a babban zabe mai zuwa a 2027.
Primate Ayodele ya ce da Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben watan Fabrairun 2023, ya hade da Atiku Abubakar na PDP da bai fadi zaben ba.
Kamar yadda malamin addinin ya bayyana, idan Obi ya yanke shawarar sake takara a zaben 2027, kawai 'bata kudinsa zai yi'.
Asali: Legit.ng