Abin da Tinubu Ya Fadawa Hadimai Jim Kadan da Kotu ta ba Shi Nasara a Shari’ar Zabe

Abin da Tinubu Ya Fadawa Hadimai Jim Kadan da Kotu ta ba Shi Nasara a Shari’ar Zabe

  • Na-kusa da Bola Ahmed Tinubu sun burma ofishinsa bayan jin nasarar da ya samu a kan jam’iyyun hamayya a kotun koli
  • Masu aiki da Shugaban Najeriyan sun yi farin ciki da sakamakon shari’ar zabe, shi kuma ya fada masu mukamansu sun tsira
  • Kotu ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin halataccen shugaban Najeriya, aka yi waje da karar Atiku Abubakar da Peter Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi farin ciki da sakamakon kotun koli a shari’ar zaben shugaban kasa inda ya doke PDP da LP.

A wani bidiyo da ke kafofin sadarwa na zamani, an ga mukarrabai da sauran masu taimakawa shugaban kasar su na murna a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

Tribune ta ce masu aiki da Bola Ahmed Tinubu sun shiga ofishinsa domin taya sa farin cikin nasarar da ya samu a shari’ar kotun koli.

Tinubu a ofis
Bola Tinubu bayan nasarar kotun koli Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukamai sun tabbata a Aso Rock

Ganin ta tabbata shi zai yi mulki na tsawon shekaru hudu, Bola Tinubu ya sanar da hadiman na sa cewa kujerarsu ta na nan daram.

"Kujerunku sun kubuta" - Bola Tinubu

Idan da jam’iyyar PDP ko LP ta yi nasara a kotu, za a iya fatattakan shugaban kasa daga Aso Rock, wani ya zo da mutanensa na dabam.

Wadanda su ka taya Tinubu murna

Hadiman da ke cikin bidiyon sun hada da Victor Adeleke (SCOPE) da mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai, Ajuri Ngelale.

Akwai Dogarin shugaban Najeriyan (ADC), Laftanan Kanal Nurudeen Yusuf da wasu jami’an tsaro da sauran masu rike da mukamai.

Kara karanta wannan

“Dadina Da Gobe Saurin Zuwa”: Kalaman Mawaki Rarara Sun Tayar da Kura a Tsakanin Yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta hangi CP Usman Musa Shugaba wanda shi ne CPSO a Aso Villa.

Rahoton ya ce Mai girma Tinubu ya fara fadawa Cif Ajuri Ngelale cewa ya tsira da kujerarsa na watsa labarai da kuma hulda da jama'a.

Tinubu: Shekaru 4 sun tabbata a Aso Rock

Daga nan sai babban Dogarin ya yi magana a madadin kowa, yake cewa sun zo ne domin su taya shugaban Najeriya murnar yin nasara a kotu.

Laftanan Kanal Nurudeen Yusuf ya kira Tinubu da Janar mai tauraro biyar wanda daukacin rundunar tsaron Najeriya ta na karkashin kulawarsa.

Daga nan aka yi gajerar addu’a, kowa ya watse a ofishin. Bidiyon ya nuna Tinubu ya na tsakiyar aiki ne a lokacin da hadimansa su ka burmo.

Tarihin shari'ar zaben shugaban kasa

Ku na da labari cewa duk da zaben da aka fi maida hankali a kai shi ne na shugaban kasa, har yau ba a taba samun kotu ta rusa wani sakamako ba.

Daga 1979 zuwa yanzu, an yi shari’ar zaben shugaban kasa da-dama, a 2003, 2007, 2011, 2019 sai kuma a bana (2023), amma duk labarin daya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng