Majalisa Ta Gamu da Matsifa Yayin da Mabarata Ke Damunsu da Rokon Kudi, Za Su Dauki Mataki

Majalisa Ta Gamu da Matsifa Yayin da Mabarata Ke Damunsu da Rokon Kudi, Za Su Dauki Mataki

  • Majalisar wakilai ta koka ganin yadda mabarata da maroka ke yawan cika harabar majalisar
  • Isma’il Haruna da ke wakiltar mazabar Toro shi ya bayyana haka yayin zaman majalisar
  • Haruna ya ce marokan na cika musu ofisoshi don rokan kudade wanda hakan ke kawo cikas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja – Majalisar Wakilai ta koka kan yadda mabarata ke damunsu a harabar majalisar da kuma cikin ofisoshinsu.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Toro, Isma’il Haruna ya ce mabarata da maroka sun hana su sakat yayin da su ke ofisoshinsu a majalisar.

Mabarata na damun majalisar wakilai da rokon kudade a Abuja
Majalisa Ta Yi Martani Kan Mabarata da Ke Damunsu da Roko. Hoto: NASS TV.
Asali: Facebook

Meye majalisar ke cewa kan mabarata da maroka?

Haruna ya ce wannan matsalar ta na shafar ayyukansu na al’umma wanda a kullum sai sun ci karo da mabaratan wadanda ke rokon kudade ba kakkautawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa Sun Hana Yafewa Talaka Biyan NECO, JAMB da WAEC Kan Tsadar Rayuwa

Dan majalisar ya bayyana haka ne yayin da ya ke magana a dakin majalisar a jiya Alhamis 26 ga watan Oktoba a Abuja, TheCable ta tattaro.

Ya ce wannan matsala ta fara wuce gona da iri ganin cewa aiki su ke zuwa yi ba raba kudade ga wasu maroka ba.

Ya ce:

“Mabaratan su na cika harabar majalisar, mu na ganin mutane daban-daban maroka da mabarata da ke cika mana ofisoshi.
“Idan za ka fita daga majalisar, wadannan mutane za su zagaye ka, don kawai su roki kudi ba kakkautawa.”

Haruna ya kuma yi korafi kan masu tasi da ke kawo cinkoso a mashigar majalisar wanda ke hana su shige da fice a majalisar.

Wane martani kakakn majalisar ya yi kan maroka?

Ya kara da cewa:

“Direbobin tasi na ‘Bolt’ da ‘Uber’ su na kawo mana cinkoso a harabar majalisar wanda hakan ke hana mu sakat.
“Su na zuwa don sauke fasinjoji da kuma daukar wasu, matsalar su na tsayawa har sai sun samu mai komawa su dauka.”

Kara karanta wannan

"Kun Saka Mana Ido, Ministoci Fa?", Majalisa Ta Kare Kanta Kan Karbar Motocin Alfarma

Yayin da Haruna ke magana, kakakin majalisar ya dakatar da shi inda ya ce ya kamata ya gabatar a matsayin kuduri ne a gaban majalisar.

Majalisar ta gayyaci gwamnan CBN don karin haske

A wani labarin, majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan CBN, Yemi Cardoso don yin bayani kan dokar shigo da kayayyaki.

CBN a kwanakin baya ta kawo wani tsari da ta haramta ba da dala a kan wasu kayayyaki 43 a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.