Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Wamakko a Matsayin Sanatan APC

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Wamakko a Matsayin Sanatan APC

  • Sanata Aliyu Wamakko ya tsallake rijiya da baya yayin da kotun zabe ta yanke hukunci kan zaben da aka gudanar a watan Faburairu
  • Kotun ta yi watsi da karar tsohon mataimakin gwamna a jihar, Manir Dan’iya na jam’iyyar PDP kan rashin gamsassun hujjoji
  • Sanata Wamakko shi ne ke wakiltar Sokoto ta Arewa a majalisar Dattawa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Sokoto – Kotun sauraran kararrakin zaben ‘yan majalisu ta yanke hukunci kan zaben Sanata Aliyu Wammako na jihar Sokoto.

Kotun ta yi fatali da korafe-korafen tsohon mataimakin gwamna, Manir Dan’iya na jam’iyyar PDP mai adawa a kasar.

Kotu ta tabbatar da nasarar Wamakko a matsayin wanda ya lashe zabe a Sokoto
Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Wamakko. Hoto: Sanata Wamakko Aliyu.
Asali: Depositphotos

Wane hukunci kotun ta yanke kan Wamakko?

Wamakko na wakiltar Sokoto ta Arewa karkashin jam’iyyar APC mai mulki yayin da Dasuki ke jam’iyyar PDP, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Ganduje Ya Bayyana Shekarar da Ya Kamata Atiku da Peter Obi Su Yi Takarar Shugaban Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a, Josephine Oyefeso a madadin sauran alkalan ta tabbatar da zaben Wamakko tare da fatali da korafe-korafen.

Oyefeso ta ce masu korafin ba su iya kawo kwararan hujjoji ba wadndaa za su gaskata bukatar su ta rushe zaben, cewar Channels TV.

Ta ce shaidun da aka gabatar ba su gamsar da kotun ba da har za su rusa hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta yanke lokacin zaben.

Wasu kararraki aka yanke hukunci bayan na Wamakko?

Dan’iya yayin gabatar da kara ya ce Wamakko bai cancanci tsayawa takara ba yayin da ya gaza ba da takardun karatunshi ga hukumar zabe.

A wata shari’ar har ila yau, dan takarar jam’iyyar APC, Bala Kokani ya kalubalanci zaben Abdussamad Dasuki na PDP kan zargin rashin samun mafi yawan kuri’u a zaben.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

Dasuki na wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Faburairu, Daily Brief ta tattaro.

Kokani ya bukaci kotun ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe inda ya ce shi ne ya samu ingantattu kuma mafi yawan kuri’u a zaben da aka gudanar.

Kotun ta yi hukunci kan zaben Tambuwal

Kun ji cewa, kotun kararrakin zabe ta yi hukunci kan zaben Sanata Aminu Waziri Tambuwal a jihar Sokoto.

Kotun ta tabbatar da Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a jihar Sokoto da aka gudanar a watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.