Ana Tsaka da Murnar Nasarar Tinubu, Babban Jigon APC Ya Rasu a Hatsarin Jirgi a Bayelsa

Ana Tsaka da Murnar Nasarar Tinubu, Babban Jigon APC Ya Rasu a Hatsarin Jirgi a Bayelsa

  • Wani ibtila'i ya afka wa jam'iyyar APC a jihar Bayelsa yayin da daraktan midiya na kwamitin kamfe, Terry Tukuwei ya nutse a ruwa tsawon awanni 10
  • Rahoto ya nuna cewa Mista Tukuwei ya nutse a ruwa ne yayin da jirgin da suka hawo ya kife a hanyar zuwa Okoroba
  • An ce marigayin na tare da tawagar likitoci na kwamitin kamfe daga garin Nembe zai kaisu ƙauyen Okoroba wurin kamfen APC

Jihar Bayelsa - Allah ya yi wa daraktan midiya na kwamitin kamfen jam'iyyar APC a jihar Bayelsa, Mista Terry Tukuwei, rasuwa sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya rutsa da shi.

Kamar yadda jaridar Tribune Online ta tattaro, haɗarin ya rutsa da jigon APC ne ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, 2023.

Daraktan midiya ya mutu a hatsarin jirgi.
Zaben Bayelsa: Daraktan Yakin Neman Zaben APC Ya Mutu a Hadarin Jirgin Ruwa Hoto: Ifeomaohiriblog
Asali: Facebook

An tattaro cewa ibtila'in ya faru ne lokacin da marigayi Tukuwei ke kan hanya daga garin Nembe zuwa ƙauyen Okoroba, ƙaramar hukumar Nembe domin halartar kamfen APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Kamfe Bayan Hatsarin Jirgin Ya Rutsa da Wasu Jiga-Jiganta

Yadda hatsarin ya faru

Ganau sun ce kwale-kwalen ya kife ne bayan da direban ya rasa yadda zai yi da shi sa'ilin da igiyar ruwa ta kawo masu cikas da misalin karfe daya na tsakar rana, ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Tukuwei na tare da wasu 'yan jarida guda biyu a cikin jirgin ruwan mai tsala gudu ɗauke da tawagar likitocin kamfen dan takarar gwamna na APC, Timipre Sylva a lokacin da hatsarin ya faru.

Ɗaya daga cikin 'yan jaridan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Mun hau jiragen ruwa daban-daban masu tsala gudu daga Nembe, lokacin da muka isa Okoroba mun sha jira na awanni amma bai ƙariso ba. Da farko mun yi tunanin ko sun tsaya a hanya ne."
"Daga baya aka gaya mana ai jirgin da ya ɗauko daraktan midiya ya kife kuma har yanzu ba a gano gawarsa ba. A bayanan da muka samu rigar ruwan ta masa ƙadan, ya gaza buɗe ta shiyasa ya nutse."

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Lakume Shaguna 7 da Dukiyar Naira Miliyan 25 a Wata Babbar Kasuwa, Gwamna Ya Yi Martani

Shugaban Matasan PDP Ya Shiga Babbar Matsala

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugaban matasanta na jihar Ondo jim kaɗan bayan rashin nasarar Atiku Abubakar a Kotun ƙoli.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, PDP reshen jihar ta umarci ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa domin a bincike shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262