Sarki da Gwamna Sun Yi Musayar Yawu Kan Alawus Din N28,000 a Bayelsa

Sarki da Gwamna Sun Yi Musayar Yawu Kan Alawus Din N28,000 a Bayelsa

  • Musayar yawu ya shiga tsakanin wani babban Sarki da gwamnatin jihar Bayelsa kan kuɗin da ake ba Sarakuna duk wata
  • Sarkin ya yi zargin cewa N28,000 kacal gwamnatin Diri na PDP ke bai wa manyan Sarakuna a wata a matsayin alawus
  • Amma gwamnatin ta bakin kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu ta maida martani kan ikirarin

Jihar Bayelsa - Sarkin masarautar Opokuma da ke ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar Bayelsa, HRM King Collins Aranka, ya koka kan kuɗin alawus din wata-wata.

Basaraken mai martaba wanda ake wa laƙabi da Ibedaowei na Opokuma ya yi zargin cewa N28,000 kacal Gwamnatin jihar take ba manyan Sarakuna duk wata.

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri.
Musayar yawu ya barke tsakanin Sarki mai daraja ta farko da gwamnatin Bayelsa Hoto: Douye Diri
Asali: UGC

Ya ce abun takaicin ana baiwa manyan sarakuna masu daraja ta farko waɗan nan kuɗaɗen a matsayin alawus na wata duk da tsadar rayuwar da ake ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan Kafa Rundunar Tsaro, Gwamnatin Radɗa Ta Yi Magana Kan Yiwuwar Tattaunawa da 'Yan Bindiga

Sarkin ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin da ya karɓi baƙuncin ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, Chief Timipre Sylva, da tawagarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma koka da yadda gwamnatin jihar Bayelsa ba ta kula da iyayen ƙasa watau sarakuna yadda ya kamata.

Gwamna mai ci kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Douye Diri, ya fito daga karamar hukumar Kolokuma/Opokuma, inda Sarkin ke jagoranta.

Gwamnatin Diri ta maida martani ga Sarkin

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta wannan ikirari, inda ta ce ana baiwa sarakunan gargajiyar jihar fiye da Naira 28,000, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Bayelsa, Cif Thompson Amule, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya ce:

"Ya dace a bayyana gaskiyar cewa Gwamnatin Jihar Bayelsa na biyan Sarakuna masu daraja ta daya a da suka kai matsayin Sarki Aranka kudi N650,000 duk wata."

Kara karanta wannan

An Gano Asusun Banki Fiye Da 570 Da Tsohon Gwamnan PDP Ya Ɓoye Kafin Ya Sauka Mulki a Arewa

“Sarakuna masu daraja ta biyu suna karbar Naira 120,000, Sarakuna na uku suna karbar Naira 80,000 yayin da ake biyan Sarakuna masu daraja ta hudu Naira 30,000 duk wata."

"Abin da Ya Sa Ya Fice Daga Zauren Majalisa Bayan Akpabio Ya Katse Ni" Ndume

A wani rahoton na daban kuma Sanata Ali Ndume ya bayyana asalin dalilin da ya sa aka ga ya fice daga zauren majalisar dattawa ana tsaka da zama ranar Talata.

Rahoto ya nuna cewa Ndume ya tattara kayansa ya bar zauren bayan Sanata Akpabio ya hana shi damar yin magana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel