An Shawarci Atiku da Obi Kan Abin da Ya Kamata Su Yi Bayan Koytun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Tinubu

An Shawarci Atiku da Obi Kan Abin da Ya Kamata Su Yi Bayan Koytun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Tinubu

  • Jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Festus Keyamo ya mayar da martani kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke
  • Kotun ƙolin dai ta yanke hukuncin tabbatar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasan Najeriya
  • Keyamo ya buƙaci waɗanda suka sha kaye a zaɓen da su gaggauta kiran Shugaba Tinubu domin ta taya shi murna a matsayinsu na ƴan kishin ƙasa

FCT, Abuja - Festus Keyamo (SAN), ministan sufurin jiragen sama, ya buƙaci Atiku Abubakar da Peter Obi da su kira Shugaba Bola Tinubu su taya shi murna bayan kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaɓe.

Atiku Abubakar da Peter Obi sune ƴan takarar shugaban kasa na jam'iyyun PDP da Labour Party (LP).

An ba Atiku da Peter Obi shawara
An bukaci Atiku da Obi su ta ya Tinubu murnar nasara a kotun koli Hoto: Atiku Abubakar, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

"Ku nuna ku masu kishin ƙasa ne': Keyamo ga Atiku, Obi

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Yi Watsi da Bukatar Atiku Ta Shigar da Sabbin Hujjoji Kan Tinubu

Keyamo ya yi nuni da cewa kiran Shugaba Tinubu da za su yi, zai nuna cewa su ƴan ƙasa ne nagari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, ministan ya nemi ƴan Najeriya da su haɗa kawunansu domin ganin an ciyar da ƙasar nan gaba.

Keyamo ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

A kalamansa:

"Hukuncin da kotun ƙoli ta yanke a yau, ya nuna ƴan baranda da ke yawo a soshiyal midiya za su gane cewa akwai bambanci mai girma tsakanin abin da zuciya ke so da doka.
"Waɗannan su ne ƙararrakin zaɓe da yawancin waɗanda ke da hannu a ciki suka riƙa amfani da tsana da ƙiyayya. A yau sun koyi darasi mai ɗaci cewa irin wannan tsanar da ƙiyayya da son rai ba su da gurbi a fannin shari'a da tattaunawa. Komai ya zo ƙarshe.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? Gaskiya Ta Bayyana

“Mun sha yin irin waɗannan kalamai ga ƴan adawa, amma sai suka cigaba da ba magoya bayansu fata na ƙarya, suna ɗora su kan hanyar da ba ta dace ba. Alƙalan mu koda yaushe a natse suke cikin ƙwarin gwiwa, jinjina garesu. Abin da ya rage yanzu shi ne gina ƙasa."
"Dole yanzu sauran ƴan takarar shugaban ƙasar su kira Shugaba Tinubu su ta ya shi murna a matsayin ƴan ƙasa nagari. Mu a matsayinmu na ƴan ƙasa na gari dole ne mu haɗa kanmu domin taimakawa wajen ciyar da ƙasar mu gaba. Ina yi mana fatan alkhairi."

Reno Omokri Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Koli

A wani labarin kuma, Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Reno ya cika da murna kan rashin nasarar da Peter Obi ya yi, inda ya ce tsohon gwamnan na jihar Anambra ba zai taɓa zama shugaban ƙasa Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng