"A Hankali Mu Na Rikidewa Zuwa Lalatacciyar Jam'iyar PDP", Jigon APC Ya Soki Shugabancin Jam'iyyar

"A Hankali Mu Na Rikidewa Zuwa Lalatacciyar Jam'iyar PDP", Jigon APC Ya Soki Shugabancin Jam'iyyar

  • Jigon jam’iyyar APC ta kasa, Salihu Lukman ya caccaki tsarin jam’iyyar inda ya ce a hankali su na lalacewa zuwa jam’iyyar PDP
  • Lukman shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar a Arewa maso Yamma ya koka kan yadda APC ke gudanar da mulkinta
  • Ya bukaci shugabannin jam’iyyar su farka daga baccin da su ke yi tare da goyon bayan shugaban kasa, Tinubu

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya ce jam’iyyar a hankali ta na rikidewa zuwa PDP.

Salihu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Laraba 25 ga watan Oktoba inda ya ce jam’iyyar ta kamo hanyar lalacewa kamar PDP a kasar.

Lukman ya soki jam'iyyar APC inda ya ce su na kara lalacewa kamar PDP
Jigon APC ya yi martani kan rugujewar jam'iyyar kamar PDP. Hoto: Abdullahi Ganduje, Lukman Salihu.
Asali: Facebook

Meye Lukman ke cewa kan APC?

Lukman ya ce abin takaici ne yadda jam’iyyar da ake mata ganin na ma su son ci gaba ta fara aiwatar da wasu abubuwa na kama-karya musamman a sama, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Fadawa Abba Gida Gida Ya Shirya, APC Za Ta Karbe Mulkin Kano a Kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shugabannin jam’iyyar da su ke ganin kansu a matsayin ma su son ci gaba ya kamata su bai wa ko wane bangare na jam’iyyar dama.

Ya ce:

“Maganar gaskiya, kasancewar APC bayan shekaru 10 da kafuwa da kuma mulkin shekaru takwas ta fara sauya kama zuwa lalacewa irin na PDP.
“Abin takaici ne jam’iyyar da ta ke kiran kanta ta ma su son ci gaba amma kuma ta na aikata wasu abubuwa na kama-karya a ayyukanta.
“Dukkan abubuwan za a iya kwatanta su da bai wa ko wane bangare na jam’iyya damar ba da gudunmawa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar.”

Wane gargadi Lukman ya yi wa APC?

Lukman ya ce jam’iyyar har zuwa yau ba ta yi wa ‘yan kasar abin da su ke tsammani ba tun bayan kafuwarta a shekarar 2013, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kotun Koli Ta Fadi Ranar Yanke Hukunci a Karar Tinubu v Atiku da Obi

Ya kara da cewa:

“Ta yaya a matsayin jam’iya mu ka yi abin kirki, ta yaya za mu gabatar da wata sabuwar manhaja na shugabanci, ko kuma dai kawai mu na komawa PDP a matsayin APC?.”

APC ta kaddamar da kwamitin kamfe a Imo

Kun ji cewa, jam’iyyar APC karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje ta kaddamar da kwamitin kamfe a jihar Imo.

Wannan na zuwa ne yayin da shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar a watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.