Atiku, Obi vs Tinubu: Abubuwa 5 da Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci a Kansu

Atiku, Obi vs Tinubu: Abubuwa 5 da Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci a Kansu

FCT, Abuja - Kotun koli ta tsayar da ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba domin yanke hukunci kan ƙararraki biyu da aka ɗaukaka da ke neman soke zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Idan dai ba a manta ba a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba ne kotun koli ta fara sauraron ƙararrakin da ƴan takarar jam'iyyun adawa suka shigar na soke hukuncin kotun zaɓe da ke tabbatar da nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zaɓen watan Fabrairu.

Kotun koli za ta yanke hukunci kan kalubalantar nasarar Tinubu
Atiku da Obi na kalubalantar nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023 Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ƴan takarar da ke ƙalubalantar zaɓen dai su ne Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP).

A yau Alhamis ne ake sa ran alƙalan kotun ƙolin su bakwai za su yanke hukunci kan waɗannan ƙararrakin.

Ga wasu muhimman batutuwan da ƴan adawa suke ƙalubalantar zaɓen saboda su:

Kara karanta wannan

Cikakkun Bayanai Kan Alkalan Kotun Koli 7 da Za Su Yanke Hukunci Kan Kararrakin Atiku da Peter Obi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1) Cancantar takarar Tinubu da Shettima

Ƴan adawa na ƙalubalantar cancantar Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Hakan ya ginu ne bisa zargin cewa Shettima ya tsaya takara sau biyu a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar sanata a lokacin zaɓe ɗaya.

Tinubu a lokacin da yake miƙa fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a watan Yunin 2022, ya zaɓi Ibrahim Masari, ɗan siyasa daga jihar Katsina, a matsayin mataimaki na wucin gadi.

Masari ya riƙe muƙamin inda daga baya ya bayyana janyewarsa, wanda hakan ya ba Tinubu damar bayyana Shettima a matsayin abokin takararsa a ranar 10 ga Yulin 2022.

2) Kaso 25% a FCT

Lauyoyin Obi sun yi zargin cewa Tinubu bai samu kaso 25% na ƙuri’un da aka kaɗa a babban birnin tarayya (FCT) ba, wanda a cewarsu, yana nufin bai cika ƙa'idar da doka ta tanada ba a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Aminu Tambuwal a Matsayin Sanata PDP

A tsarin dokar zaɓe ta Najeriya, ɗan takarar shugaban ƙasa yana yin nasara ne idan ya samu kaso ɗaya bisa huɗu na ƙuri'un da aka kaɗa a akalla kaso biyu bisa uku na dukkanin jihohi 36 da Abuja.

Ƴan adawa da lauyoyin Tinubu sun yi wa wannan tanadin fassara daban-daban.

3) Zargin INEC ba ta yi amfani da na'uar IreV ba

Atiku da Obi sun yi zargin cewa INEC ta gudanar da zaɓen 2023 ne bisa rashin gaskiya.

A cewar ƴan takarar jam'iyyun adawa, lauyoyinsu, da magoya bayansu, zargin rashin gaskiyar da INEC ta yi ya saɓa wa dokar zabe ta 2022.

Suna zargin gazawar INEC wajen sanya sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe zuwa kan na'urar IReV, wacce ke nuna sakamako kai tsaye.

4) Zarge-zargen yin maguɗin zaɓe saboda da Tinubu

Atiku ya zargi INEC da sanya wata na'ura domin yin maguɗin zaɓe saboda Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Fintiri Vs Binani: Magana Ta Kare, Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Sahihancin Zaben Gwamnan Adamawa

Hakazalika, jam'iyyar Atiku, PDP, sun zargi shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a watan Fabrairu.

5) Takardun karatun Tinubu da aka samu daga CSU

Alƙalan kotun ƙoli na son Atiku ya tabbatar da zargin yin jabun satifiket da ake yi wa Shugaba Tinubu ba tare da wata shakka ba.

A yunƙurinsa na soke nasarar Tinubu da tabbatar da zargin cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa ba, Atiku ya nemi wata kotun gundumar Illinois a Chicago, da ta umurci jami'ar jihar Chicago (CSU) ta saki bayanan karatun Shugaba Tinubu.

Daga baya jami'ar CSU ta bayar da takardu uku cikin huɗu waɗanda tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nema.

Jigon PDP Ya Nemi Kotun Koli Ta Kori Tinubu

A wani labarin kuma, wani jigo a jam'iyyar PDP ya buƙaci kotun ƙoli da ta kori Shugaba Tinubu daga muƙamin shugaban ƙasa.

Abdul'aziz Na'ibi Abubakar ya kuma buƙaci kotun ƙolin da ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng