Tinubu Ya Nada Sabbin Kwamishinonin Zaben Jihohi 9 a Najeriya
- Shugaba Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin zaben jihohi guda tara a Najeriya
- Tinubu ya yi wannan nadin ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a wasu jihohi uku a watan gobe
- Hadimin shugaban a bangaren yada labarai ta zamani, David Olusegun shi ya bayyana haka a shafinsa na twitter
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin zabe a jihohi tara a Najeriya.
Tinubu ya yi nadin ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabukan jihohi a Kogi da Imo da Bayelsa a watan Nuwamban wannan shekara, Legit ta tattaro.
Su waye Tinubu ya nada mukamai a hukumar zabe?
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai ta zamani, David Olusegun shi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a yau Laraba 25 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda aka nadan akwai:
Mista Isah Shaka Ehimeakne - Kwamishinan zaben jihar Edo
Mista Bamidele Agbede — Kwamishinan zaben jihar Ekiti
Jani Adamu Bello — Kwamishinan zaben jihar Gombe
Dakta Taiye Ilayasu — Kwamishinan zaben jihar Kwara
Dakta Bunmi Omoseyindemi — Kwamishinan zaben jihar Lagos
Alhaji Yahaya Bello — Kwamishinan zaben jihar Nasarawa
Farfesa Mohammed Yalwa — Kwamishinan zaben jihar Niger
Dakta Anugbum Onuoha — Kwamishinan zaben jihar Ribas
Abubakar Fawa Dambo — Kwamishinan zaben jihar Zamfara
Meye sanarwar ta ce kan nadin Tinubu a hukumar zabe?
Sanarwar ta ce:
"Bisa dokar da ta ba shi dama a sashi na 154 na cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ta shekarar 1999.
"Shugaba Tinubu ya nada sabbin kwamishinonin zaben jihohi tara na Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC na tsawon shekaru biyar.
"Nadin dukkan kwamishinonin ya ta'allaka ne ga tabbatar da su da majalisar Dattawa za ta yi."
A cikin wannan wata kadai Shugaba Tinubu ya yi nade-naden mukamai da dama a gwamnatinsa.
Sai dai jama'a da dama na sukar nadin da cewa son kai ya yi yawa a ciki.
Tinubu ya nada shugabannin hukumomin NIWA, NSC
A wani labarin, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada shugabannin hukumomin NIWA da NSC da e karkashin ma'aikatar Albarkatun Ruwa.
Tinubu ya yi nadin ne bayan sahalewar ministan ma'aikatar, Adegboyega Oyetola.
Shugaban ya nada Munirudden Bola a matsayin daraktan NIWA yayin da Akutah Ukeyima ya zama babban daraktan hukumar NSC.
Asali: Legit.ng