Takarar Gwamnan Kogi Ta Dauki Zafi, An Bugi Shugaban Jam’iyya Ya Daina Shura Wa

Takarar Gwamnan Kogi Ta Dauki Zafi, An Bugi Shugaban Jam’iyya Ya Daina Shura Wa

  • ‘Yan bangar siyasa ake zargin sun shiga kauyen Aja-Odi Agojoeju da ke karamar hukumar Ofu, sun lallasa jagora a SDP
  • Ana tunanin an yi wa Fasto Sunday Atabo dukan tsiya, har ta kai ya na kwance a gadon asibiti ko motsi bai iya yi a halin yanzu
  • Shugabannin jam’iyyar SDP sun yi bayanin yadda aka yi barna a gidan Sunday Atabo, aka kuma nemi a kona gidan kurmus

Kogi - Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kai hari a gidan daya daga cikin jagororin jam’iyyar adawa ta SDP a jihar Kogi.

Daily Trust ta ce ‘yan iskan garin sun aukawa Fasto Sunday Atabo a gidansa da ke kauyen Aja-Odi Agojoeju a karamar hukumar Ofu da ke jihar.

Yanzu haka Fasto Sunday Atabo wanda shi ne shugaban shiyyar jam’iyyar SDP a Kogi ya na kwance a gadon asibiti a sakamakon mugun harin.

Kara karanta wannan

Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Fuskantar Barazana

Kogi.
Taron takarar Gwamna a jihar Kogi Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Siyasa ta jawo an doke Fasto a Kogi

Wani da ya shaida abin da ya faru a ranar Asabar, ya ce ‘yan bangar siyasar sun shigo gidan wannan mutum dauke da AK-47, adda da karafuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga zamansa ‘dan siyasa, rahoton ya ce Sunday Atabo shi ne babban limamin cocin Bible Believers da ke Agojeju-Efakwu a garin na Ofu.

Zuwa yanzu an kwantar da shi a asibitin da ba a iya bayyanawa duniya ba, ya na jinya, a wata majiyar an ji Faston bai san inda yake ciki ba.

An kusa kona gidan shugaban SDP

Sakataren SDP, Dr Arome Okeme ya ce an yi yunkurin kona gidan wannan Bawan Allah bayan an tarwatsa motoci da dukiyoyin da ke ciki.

Darektan yada labarai a kafafen zamani na kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Kogi, ID Ijele, ya yi Allah-wadai da abin da ya faru.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Arewa

A yayin da yake magana, ID Ijele ya ce an dade ana kai wa jiga-jigan SDP hare-hare.

"Manufar wannan danyen aiki ita ce a razana jagororinmu da masu zabe, har a hana su fitowa kada kuri’a a ranar zabe.
Mun saba kai karar wadannan hari, kuma za mu cigaba da yin haka, da fatan jami’an tsaro za su yi abin da ya dace domin hana aukawa mabiyanmu da ta’adi."

- ID Ijele

SDP ta yi kira ga Kwamishinan ‘yan sanda, shugaban NSCDC, DSS da na sojoji da sauran jami’an tsaro su yi bincike a kan aika-aikar da aka yi.

Shari'ar PDP v APC a kan zaben 2023

Ku na da labari Helen Moronkeji Ogunwumiju wanda ake zargin yaronta ya na APC ta na cikin Alkalan da za su saurari karar zaben shugaban kasa.

Atiku Abubakar, Peter Obi da Chichi Ojei ba su gamsa da hukuncin kotun korafi ba, 'yan takaran adawan sun daukaka zuwa kotun Allah ya isa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng