Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukuncin Shari'ar Zaben Shugaban Kasa
- Kotun koli ta shirya tsaf don ganin ta kawo karshen takaddama na shari'ar shugaban kasa
- A watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zabe ta kori karar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP
- Atiku na kalubalantar zaben Shugaba Tinubu kan tafka magudin zabe da kuma kura-kurai a hukuncin kotun
FCT, Abuja - Kotun koli ta sanar da cewa ta shirya yanke takaddama na shari'ar zaben shugaban kasa a mako mai zuwa.
Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP na kalubalantar zaben Shugaba Tinubu da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara, Legit ta tattaro.
Yaushe kotun za ta yanke hukuncin Tinubu, Atiku?
A yau Alhamis 19 ga watan Oktoba kotun kolin ta tura sanarwar ga lauyoyin masu kara da ma su kare kansu a shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun koli ta sanar da ranar Litinin 23 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin zaben shugaban kasa a Abuja, The Nation ta tattaro.
A farkon watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da korafin 'yan jam'iyyun adawa.
Kotun ta watsar da korafin 'yan takarar jam'iyyun PDP, Atiku Abubakar da Labour, Peter Obi.
Wane mataki Atiku ya dauka kan Tinubu?
Bayan yanke hukuncin, Atiku ya daukaka kara zuwa kotun koli don kwato hakkinsa da aka tauye ma sa.
A dalilin haka, Atiku ya binciko badakalar takardun Tinubu na Jami'ar Chicago da ke Amurka.
Tun farko, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci kotu ta tilasta Jami'ar mika ma sa takardun karatun Tinubu da ake cece-kuce a kansu.
Ana shi bangaren, Obi shi ma ya daukaka kara a kotun koli inda ya bukaci kotun ta yi fatali da hukuncin kotun a baya.
Kotun zabe ta yi watsi da korafin Atiku
A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa a Abuja ta yi fatali da korafin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.
Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar na kalubalantar zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Har ila yau, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi shi ma ya sha kaye bayan kotun ta yi watsi da karar da ya shigar.
Asali: Legit.ng