CAN Da JNI Sun Nesanta Kansu Daga Ikirarin Lawal Na Cewa APC Ta Zama Jam’iyyar Musulunci

CAN Da JNI Sun Nesanta Kansu Daga Ikirarin Lawal Na Cewa APC Ta Zama Jam’iyyar Musulunci

  • Kungiyoyin Musulunci da na Kirista sun yi watsi da ikirarin Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, na cewa APC ta zama jam'iyyar Musulunci yanzu
  • CAN, kungiyar kiristocin Najeriya ta ce bai kamata wani mutum ya ware jam'iyyar siyasa a matsayin ta wani addini ba
  • Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ma ta kalubalanci Lawal da ya fito ya tabbatar da ikirarinsa da hujja kan yadda APC mai mulki a kasar ta zama jam'iyyar Musulunci

Ikirarin Injiniya Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya na cewar jam'iyyar APC ta zama jam'iyyar Musulunci a yanzu ya haifar da martani daga kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) da ta Jama’atu Nasril Islam (JNI).

A ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, ne Lawal ya yi ikirarin cewa Peter Obi, dan takarar LP, ne ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu kuma cewa Shugaban kasa Bola Tinubu bai lashe zaben ba, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

APC Ta Fallasa Babachir, Ta Tona Dalilinsa na Jin Haushin Shugaba Tinubu

CAN ta ce bai kamata a danganta wata jam'iyya da addini ba
CAN Da JNI Sun Nesanta Kansu Daga Ikirarin Lawal Na Cewa APC Ta Zama Jam’iyyar Musulunci Hoto: Babachir Lawal, APC Nigeria
Asali: Twitter

A ranar Laraba, dattijon kasar ya ci gaba da caccakar jam'iyyar mai mulki da shugaban kasa Tinubu lokacin da ya yi ikirarin cewa Obi, wanda ya zo na uku a zaben, shine ainahin wanda ya lashe zaben.

CAN ta yi watsi da ikirarin Babachir Lawal cewa APC ta zama jam'iyyar Musulunci

Sai dai kuma CAN ta nesanta kanta daga danganta jam'iyyun siyasa da addini, tana mai cewa irin wannan ra’ayi ya sabawa tsarin hada kai da rashin mutunta bambancin addini a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A nata bangaren, JNI ta bukaci tsohon sakataren gwamnatin tarayyar da ya gabatar da hujja kan yadda APC, jam'iyyar kasar da jami'ai da aka zaba a fadin kasar, ta zama jam'iyyar Musulunci.

Wani babban jami'in CAN wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba daidai bane a danganta wata jam'iyyar siyasa a matsayin ta addini, yana mai cewa kungiyar kirista bata lamuncewa kowace jam'iyyar siyasa ba, rahoton Business day.

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hannun Riga Da Isra'ila": Kungiyar Musulmi Ta Aika Sako Ga Kasashen Duniya Kan Yakin Gaza

Kungiyar Musulunci ta kalubalanci Lawal kan ikirarinsa game da APC

Malam Ibrahim Kufena, sakataren kungiyar JNI reshen jihar Kaduna ya ce da sai tsohon sakataren gwamnatin ya yi karin bayani kan yadda aka yi APC ta zama jam'iyyar Musulunci.

Ya ce:

"A wani dalili ne APC ta zama jam'iyyar Musulunci? Imo, Ebonyi da sauran jihohin da akwai APC, jihohin Musulunci ne? Ko a wurare irin su Kano, duk APC suke yi?"

APC ta fallasa Babachir, ta tona abin da ya sa yake jin haushin Shugaba Tinubu

A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa jam’iyyar APC mai mulki ta maidawa Babachir David Lawal a kan ikirarin da ya yi na nasarar Peter Obi a takarar shugaban kasa.

Punch ta ce APC ta kula Injiniya Babachir David Lawal, ta na cewa ya na surutu ne saboda bai huce takaicin rasa mataimakin shugaban kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel