Atiku Ya Bukaci Kotun Koli Ta Amince da Bukatarsa Ta Gabatar da Sabbin Hujjoji Kan Tinubu

Atiku Ya Bukaci Kotun Koli Ta Amince da Bukatarsa Ta Gabatar da Sabbin Hujjoji Kan Tinubu

  • Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya sake neman kotun koli ta amince ya gabatar da sabbin hujjoji kan Bola Tinubu
  • Atiku ya buƙaci kotun da ta ba shi damar gabatar da wasu ƙarin shaidu domin ƙara tabbatar da cewa Tinubu ya miƙa takardun jabu ga INEC a lokacin zabe
  • Tsohon mataimakin ya tunatar da kotun cewa gabatar da takardun jabu daga kowane ɗan takara a lokacin zaɓe lamari ne mai matukar muhimmanci da bai kamata a kawar da kai ba

FCT, Abuja - Dan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar, ya sake neman kotun ƙoli da ta amince da buƙatarsa da bayar da izinin gabatar da ƙarin sabbin shaidu.

Tun da farƙo dai lauyoyin Tinubu dai sun buƙaci kotun ƙolin da ka da ta amince da buƙatar Atiku na gabatar da sabbin hujjoji kan takardun karatun Shugaba Tinubu na jami'ar Chicago (CSU)

Kara karanta wannan

BBC Ta Tsaya Kan Bakanta Cewa Shugaba Tinubu Bai Yi Jabun Satikifet Na Jami'ar Chicago Ba

Atiku ya garzaya kotun koli
Atiku ya kai kukansa a gaban kotun koli Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya ƙalubalanci Tinubu a kotun ƙoli

Atiku a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, ya buƙaci kotun ƙolin da ta ba shi damar gabatar da sabbin shaidu da za su goyi bayan iƙirarinsa na cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa takardun jabu ga hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a lokacin zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton jaridar The Nigerian Tribune, Atiku ya fayyace roƙonsa ne bisa hujjar cewa gabatar da takardun jabu daga kowane ɗan takara, musamman a muƙami mafi girma a ƙasa, babban lamari ne a kundin tsarin mulkin wanda bai kamata a bari ya auku ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a martanin da ya mayar kan batun doka na ƙin amincewar Tinubu na ba Atiku izinin gabatar da sabbin shaidu a gaban kotun kolin, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Kotun Koli Kada Ta Karbi Sabbin Hujjojin Atiku, Ya Bayyana Dalilansa

Babu Hujja Tinubu Ya Yi Jabun Satifiket, BBC

A wani labarin kuma, kun ji cewa kafar watsa labarai ta Burtaniya (BBC) ta wanke Tinubu kan zargin yin jabun satifiket na jami'ar jihar Chicago (CSU).

BBC a wani bincike da ta gudanar ta bayyana cewa babu hujja da ke nuna cewa shugaban ƙasar ya yi jabun satifiket na jami'ar CSU.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng