Sanata Ya Fadi Ministocin Da Shugaba Tinubu Zai Sallama Daga Ofis a 2024
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zo da sabon salon da ba a saba da shi ba, za a rika auna irin kokarin ministocinta
- Duk wani ministan da yake rike da mukami a yau zai iya rasa kujerarsa idan bai tabuka komai a watanni shida ba
- Sanata Smart Adeyemi ya ce Shugaba Tinubu ba wasa ya fito yi ba, ya kagara ya ga an fara kawo gyara a Najeriya
Abuja - Duk wani Ministan tarayya da bai yi aiki da kyau ba, zai rasa kujerarsa nan da watanni a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A yayin da tashar Arise ta yi hira da Smart Adeyemi a ranar Laraba, Sanatan ya nuna cewa za a watsar da ministocin da ba su aiki.
Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya nuna Bola Ahmed Tinubu sam ba da wasa ya zo ba.
A baya, Hadiza Bala Usman ta ce akwai ma’aunin da za ayi amfani da shi domin a rika duba kokarin da duka Ministoci su ke yi a ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abin da ‘yan Najeriya har da ministoci ya kamata su sani game da shugaban kasa Bola Tinubu a yau, shi ne, idan ba ka yi aiki cikin watanni shida ba, zai yi waje da kai.
Abin da zai yi kenan. Wannan mutumi (Bola Tinubu) ya zo da gaggawan shirin yin aiki.
Asiwaju ya na so ya bar tarihi. Ya na so ya gyara Najeriya. Ya na so ya dawo da martabar da kasar ta rasa.
- Smart Adeyemi
Vanguard ta rahoto ‘dan majalisar ya na cewa Bola Tinubu ya san da wahalar da ake ciki a daidai lokacin da ake ta kukan tsadar rayuwa.
Adeyemi ya ce Sanatoci sun san aiki
Ganin Tinubu da mai dakinsa, Remi Tinubu da Kashim Shettima tsofaffin ‘yan majalisa ne, Adeyemi ya ce dole Sanatoci su tashi tsaye.
Ganin haka ya bada misali da Hope Uzodinma wanda ya ce tsohon Sanata ne kuma yanzu gwamnatinsa ta ke kokari wajen gyara jihar Imo.
‘Yan kasuwa sun fara kuka da Tinubu
Duka-duka, sabuwar gwamnati ba ta yi wata 5 ba, amma Dala ta tserewa Naira sosai a kasuwa, an ji labari an saida $1 a kan sama da N1, 1000.
A dalilin haka wasu su ka fara tunanin a haka Gwamnati za ta farfado da tattalin arziki kamar yadda shugaban kasar ya dauki alwashi.
Asali: Legit.ng