A kori Dino: An rantsar da Smart Adeyemi a matsayin sabon Sanatan Kogi ta yamma

A kori Dino: An rantsar da Smart Adeyemi a matsayin sabon Sanatan Kogi ta yamma

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya rantsar da sabon Sanatan jam’iyyar APC dake wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Smart Adeyemi.

Smart, wanda tsohon Sanata ne a karkashin jam’iyyar PDP, a yanzu ya samu nasara ne cikin jam’iyyar APC inda ya kayar da abokin karawarsa Dino Melaye na jam’iyyar PDP, wanda a shekarar 2015 ya kwace kujerar a hannun Smart a APC.

KU KARANTA: Alaramma da ya amshi naira biliyan 1 don cusa haddar Qur’ani a kan wani ya shiga hannun EFCC

Rahoton Daily Trust ya bayyana wannan nasara ta Adeyemi ya kara yawan Sanatocin jam’iyyar APC zuwa 63, yayin da jam’iyyar PDP ke da Sanatoci 45, sai jam’iyyar YPP dake da Sanata guda daya tal!

Hukumar zabe mai zaman kanta ne dai ta sanar da Smart a matsayin halastacce kuma zababben dan majalisa bayan lashe zabe na biyu wanda ya gudana a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Idan za’a tuna, bayan kammala zaben 2019 wanda hukumar INEC ta sanar da Melaye a matsayin wanda ya samu nasara ne sai Smart ta tafi gaban kotu inda ya kalubalanci nasarar da INEC ta yi ikirarin Melaye ya samu.

Kotun sauraron koke koken zabe ta soke zaben Melaye, amma bai amince da hukuncin kotun ba, inda ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, sai dai a nan ma ya gamu da tasgaro, daga karshen shari’ar kotun ta soke zaben Melaye, sa’annan ta bada umarnin a sake gudanar da wani sabon zabe.

A kan doron wannan hukunci na kotu ne hukumar INEC ta shirya sabon zabe a ranar 16 ga watan Nuwamba a mazabar Kogi ta yamma, amma da yake zaben bai kammalu ba, sai ta karashe shi a ranar 30 ga watan Nuwamba, inda ta sanar da Smart a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai tuni Dino Melaye ya yi watsi da sakamakon wannan zabe, inda ya dauki alwashin kalubalantar nasarar Adeyemi a gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel