"Ku Yi Hannun Riga Da Isra'ila": Kungiyar Musulmi Ta Aika Sako Ga Kasashen Duniya Kan Yakin Gaza
- Bayan kusan mako guda bayan Hamas ta kai hari a Kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, Isra'ila ta rika 'ruwan bama-bamai
- Legit Hausa ta rahoto cewa Hadakar Kungiyoyin Musulunci, CIO, ta yi ikirarin cewa Isra'ila ta karya dokokin kasa da kasa na zaman lafiya
- Kungiyar mai hedkwata a Najeriya ta kuma yi tir da rashin ikon da ake zargin Majalisar Dinkin Duniya (UN), kungiyar da aka kafa domin wanzar da zaman lafiya a duniya ba ta da shi
Surulere, Jihar Legas - Kungiyar musulunci 'Conference of Islamic Organisation (CIO)', ta yi kira ga kasashen duniya su 'kwace ikon da Amurka ke da shi wurin shiga tsakanin Isra'ila da Falasdinu'.
Legit.ng ta rahoto cewa CIO ta yi ikirarin cewa Amurka na 'cikin matsalar' tana zargin Washington da nuna 'fifiko' a kan batun kutsen da Isra'ila ta yi a Gaza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gaza: Kungiyar musulunci ta mika sako ga UN
Kungiyar, wacce ta kunshi kungiyoyin musulunci daban-daban a Najeriya, ta yi wannan kiran ne a taron manema labarai da ta yi a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, a Legas.
Da ya ke magana a wurin taron, Sakataren CIO, Injiniya Lukman Balogun ya kallubalanci UN ta nemo wani hanyar 'samar da zaman lafiya na gaskiya' wanda ya ce 'zai yi la'akari da batun neman samun yancin Kasar Falasdinu.'
Rikicin Isra'ila da Falasdinu: "Abin da ya zama dole Najeriya ta yi'
Bugu da kari, kungiyar ta jinjinawa gwamnatin Najeriya saboda kiran da ta yi ga Isra'ila da Falasdinu su tsagaita wuta su rungumi zaman lafiya da sulhu. Amma ta yi kira ga majalisar kasar ta yi doka da zai rage harkokin diflomasiyya da Isra'ila 'saboda saba dokokin UN'.
APC Ta Zama Jam’iyyar Musulunci Yanzu? CAN, JNI Sun Dauki Zafi Kan Ikirarin Sakataren Gwamnatin Buhari
"Muna kira ga kasashen Larabawa, kasashen Musulmi, ciki har da gwamnatin Najeriya da shugabanni masu zurfin tunani su dauki matakan da za su tilastawa Isra'ila canja halayenta na wariyya ta fara biyaya ga dokokin kasa da kasa.
"Muna kira ga kasashen Larabawa, musamman kasashen Gabas ta Tsakiya wadanda suka kulla alaka da Isra'ila da wadanda ke niyyar hakan su dakata, don karrama yan uwansu Falasdinawa da sojojin da suka yi kutse ke yi wa kisa ba kakkautawa."
Jagoran musulmi ya ce Hamas ba yan ta'adda bane
A jawabinsa wurin taron, shugaban kungiyar (masanin shari'ar musulunci), Sheikh Dhikrullah Shafi'i ya jadada cewa Hamas, kungiyar masu ikirarin jihadi da ke da iko a Gaza, ba kungiyar ta'addanci bane 'kamar yadda kasashen Yamma ke fada'.
A cewarsa, mambobin Hamas masu yaki neman yanci ne kuma kungiya ce ta masu turjiyya da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya da ke mulkar Zirin Gaza.
Asali: Legit.ng