Ba APC Ta Ci Zabe Ba, Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Ce Peter Obi Ne Ya Yi Galaba a Zaben 2023

Ba APC Ta Ci Zabe Ba, Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Ce Peter Obi Ne Ya Yi Galaba a Zaben 2023

  • Babachir David Lawal ya fadi ra’ayinsa a game da zaben shugaban kasa da aka yi a bana, ya ce sam ba APC ta yi nasara ba
  • A wani jawabi da ya fitar, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyan ya ce Bola Tinubu ya zo bayan jam’iyyun APC da PDP ne
  • Peter Obi da Atiku Abubakar su na kotu inda su ke shari’a da Hukumar INEC, jam’iyyar APC mai mulki da ‘dan takaranta

FCT, Abuja - Babachir David Lawal, wanda ya taba zama sakataren gwamnatin tarayya a lokacin Muhammadu Buhari ya yi magana kan zaben 2023.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Talata, The Cable ta ce Injiniya Babachir David Lawal ya yi ikirarin Peter Obi ya yi nasara a zaben shugaban kasa.

‘Dan siyasar ya ke cewa Atiku Abubakar da ya yi takara a jam’iyyar PDP ne ya zo na biyu yayin da Bola Ahmed Tinubu da APC su ka kare a na uku.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

Babachir David Lawal
Yakubu Dogara, Samuel Ortom, Babachir David Lawal Hoto: @YakubDogara
Asali: Twitter

Jawabin Babachir David Lawal

"Na gujewa kwadayin tsoma baki a game da sha’anin siyasa tun bayan zaben je-ka-na-yi-kan 2023 da ya gudana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na yi wannan ne saboda dalilai biyu; na farko shi ne a matsayin wanda ke cikin masu ruwa da tsaki, ina bukatar lokaci domin in duba alkaluman da su ka kai ga sakamakon domin in yanke matsaya na ilmi; na biyu kuma saboda damina ta sauko, saboda haka ina bukatar maida hankali a game da gonaki na wanda su ne hanyar samun na abinci na.
Magana da tambayoyi a game da cancanta ko nasarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa, la’akari da kila-wa-kala game da bayaninsa ya zama abin tattaunawa a fili a kullum.
Amsa ta game da tambayar nan ita ce, duk abin da INEC ko kotun daukaka kara ta ce, Bola bai lashe zaben ba."

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kotu ta Tsige Sanatan Adamawa, ‘Dan Takaran PDP Ya Samu Nasara

- Babachir David Lawal

An rahoto Babachir Lawal ya na cewa tun da Tinubu ya shiga zabe, ya san ba zai yi nasara ba, saboda haka ya nemi wasu hanyoyin idanunsa a rufe.

Babachir: "Bola Tinubu bai da lafiya"

A cewarsa, alkaluman da ya tattara sun tabbatar masa Obi ya fi samun rinjayen kuri’u, ya yi kira ga Bola Tinubu ya yi murabus saboda lafiyarsa.

Watanni kusan shida da hawa mulki, ‘dan siyasar ya ce an fara kuka da halin da Tinubu ya jefa kasa na cika gwamnati da mutanensa na siyasa.

Korar Babachir David Lawal daga ofishin SGF

Tsakanin 2015 da 2023, an ji labarin yadda Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitocin gwamnati kimanin 40 wanda su ka tashi ba biliyoyi.

Boss Gida Mustapha da Babachir David Lawal ne su ka rike a shekaru 8 da suka wuce. Babachir ya rasa kujerarsa ne saboda zargin rashin gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng