Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP Na Jihar Kwara Ya Koma APC

Tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP Na Jihar Kwara Ya Koma APC

  • Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi asarar ɗaya daga cikin manyan jigoginta ga babbar abokiyar hamayyarta, APC
  • Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa APC ta karɓi Rasaq Lawal wanda ya taɓa zama sakataren jam'iyyar PDP a jihar Kwara
  • Lawal ya yi magana game da tsohuwar jam’iyyarsa a wani taron da jam’iyyar APC ta gudanar a hukumance domin karɓarsa zuwa cikinta

Ilorin, jihar Kwara – Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na jihar Kwara, Alhaji Rasaq Lawal, ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Legit Hausa ta fahimci cewa Lawal yayi murabus daga ofishin sa a watan Yulin 2023.

Jigon PDP a jihar Kwara ya koma APC
Alhaji Rasaq Lawal ya ce jam'iyyar PDP ba ta da tsari Hoto: @yusufalabere19
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta ce a lokacin, ya ce ya yanke shawarar yin murabus daga matsayinsa na sakataren jam’iyyar tare da ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai na ƙashin kansa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babban Jami'in PDP Na Kasa Ya Koma APC, Bayanai Sun Bayyana

Yanzu, bayan watanni uku, shugabannin APC na jihar ƙarƙashin jagorancin Sunday Fagbemi sun tarbi Lawal a hukumance a sakatariyar jam'iyyar da ke Ilorin, a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Lawal ya koma APC?

Jaridar ta kuma ce Lawal ya bayyana jin daɗinsa bisa komawa cikin jam'iyyar APC. Ya kuma yi wa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP kaca-kaca.

Kalamansa:

"Yayin da nake mutunta juna da shugabanni da takwarorina a tsohuwar jam’iyyata, ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen bayyana cewa PDP ba ta da tsari yadda ya kamata domin ta taka rawar babbar jam'iyyar adawa."
"Aikin babbar jam’iyyar adawa shi ne ta taimaka wa gwamnati mai ci ta cimma manufofinta na kawo cigaba ga al'umma, ba wai ta zama mai kawo cikas ga cimma irin waɗannan manufofin ba."

Kara karanta wannan

Da Gaske NWC Ya Kori Sakataren Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Daga Muƙaminsa? Gaskiya Ta Bayyana

Ya ƙara da cewa:

"Ina so in tabbatar wa gwamna na kuma jagoran jam'iyyar APC na jihar Kwara/ shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), shugaban jam’iyyar APC da tawagarsa gaba ɗaya na jajircewa ta wajen tabbatar da manufofin jam’iyyar da kuma cigaban gwamnatin jam'iyyar APC a jihar nan."

PDP Ta Magantu Kan Anyanwu

A wani labarin kuma, kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar PDP ya yi magana kan batun sauke Samuel Anayanwu daga muƙamin sakataren jam'iyyar ɓa ƙasa.

Kwamitin ya bayyana cewa har yanzu Anyanwu yana na daram a matsayinsa na sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng