Kotu ta Tsige Sanatan Adamawa, ‘Dan PDP Ya Yi Nasara a Kan Elisha Abbo a Kotu

Kotu ta Tsige Sanatan Adamawa, ‘Dan PDP Ya Yi Nasara a Kan Elisha Abbo a Kotu

  • Kotun daukaka kara ta rusa zaben da ya ba Sanata Elisha Ishaku Abbo nasarar komawa majalisar dattawan Najeriya a 2023
  • Rabaren Amos Yohanna na jam’iyyar PDP ya kalubalanci ‘Dan majalisar na Adamawa ta Arewa, ya ce bai ci zabe a APC ba
  • Lauyan ‘dan takaran jam’iyyar PDP ya fadawa kotu cewa Hukumar INEC ba ta bi ka’ida da dokar zabe kamar yadda aka tsara ba

Abuja - Kotun sauraron daukaka kara da ke zama a garin Abuja, ya soke zaben Elisha Ishaku Abbo da aka yi a farkon 2023.

Rahoton da aka samu daga tashar Channels TV a yammacin Litinin ya ce Sanata Elisha Ishaku Abbo bai yi nasara a kotu ba.

Sanatan na Adamawa ta Arewa ya gamu da cikas ne a sakamakon karar da Amos Yohanna ya shigar a kan zaben na bana.

Kara karanta wannan

Gaza: Saudiyya Ta Kira Taron Musulmai, Fafaroma Ya Tsawata Wa Isra'ila

Sanatan Adamawa
Sanata Elisha Abbo Hoto: @IDomiya
Asali: Twitter

Sanatan APC bai ci zabe ba?

Rabaren Amos Yohanna ya yi ikirarin an sabawa dokar zabe wajen ba Elisha Abbo da APC nasara a zaben ‘dan majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da ya fara zuwa shi ne malaman addinin kuma fasto da ya yi takara a PDP mai mulki a Adamawa ya yi nasara a kotu.

Za a saurari cikakken hukuncin da Alkalan su ka gabatar a Abuja. Kotun daukaka kara ne makura wajen shari’ar zaben majalisa.

Shari'ar zaben 2023

A karamin kotun karar zabe, Mai shari’a Aloysius Okuma ne ya saurari karar Yohanna da Abbo wanda ya ke majalisa tun 2019.

Lauyoyin ‘dan takaran PDP sun ce ba jam’iyyar APC ta samu rinjayen kuri’un Adamawa ta Arewa a zaben da aka yi a Fabrairu ba.

Jerry Owe wanda ya tsayawa ‘dan siyasar a lokacin ya yi ikirarin an soke kuri’u masu yawa a zaben ba tare da an bi ka’ida ba.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar APC Ya Tona Abin da Ya Hana Kawo Karshen Rashin Tsaro a Arewa

Lauyan APC ya sha kashi a kotu

A hujjojin abokin adawar na Abbo, akwai zargin cewa wakilan jam’iyyar PDP ba su rattaba hannu a takardun sakamakon zaben ba.

Kafin shiga takarar 2023, Sanata Abbo ya yi ta fuskantar kalubale, har an nemi kotu ta hana shi tsayawa neman kujerar majalisa.

Shi kuwa Sanatan ya dauko hayar babban lauya, Sam Ologunorisha (SAN) ne domin ya kare shi da kujerar da yake sa ran sauka a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel