Abubuwa 6 da baku sani ba dangane da sanata mai saurin hannu, Elisha Abbo

Abubuwa 6 da baku sani ba dangane da sanata mai saurin hannu, Elisha Abbo

Daga ranar Laraba, 2 ga watan Yuli zuwa Alhamis, 3 ga watan Yuli, sunan Sanata Elisha Abbo ya zama ruwan dare a fadin Najeriya, musammam a wurin ma'abota amfani da dandalin sada zumunta.

Sanata Abbo ya shiga bakin 'yan Najeriya da ma duniya baki daya bayan ya mammari wata mata mai jego a wani shagon sayar da kayan batsa a Abuja.

Ga wasu abubuwa guda biyar da ba lallai kun sani ba a kan Ssanata Abbo

1. Shine sanata mafi karancin shekaru a majalisar dattijai ta tara ba, ya na da shekara 41 a duniya

2. Ya taba shigar da karar kwalejin horon sojojin ruwa da ke garin fatakwal saboda sun ki daukansa bisa hujjar cewa bashi da koshin lafiya.

3. An nadi faifan bidiyonsa yayin da ya ke cin zarafin wata mata a wwani shagon sayar da kayan batsa a Abuja bisa zargin cewa matar ta kira shi bugagge.

4. Duk da ya fito daga yanki mai yawan Musulmi a jihar Adamawa, sanata Abbo kirista ne da ya yi imani Yesu almasihu da koyarwar littafin Injila

5. Ana ta samun kiraye-kiraye daga sassa da kungiyoyi daban-daban a kan a kama shi tare da gurfanar da shi bayan faifan bidiyon marin da ya yi wa matar ya fantsama a dandalin sada zumunta da kafafen yada labarai.

6. Matarsa, Emily Eric, ta fito fili ta kare shi duk da irin shaidar da aka nuna a kan cin zarafin matar da ya yi.

Emily ta rubuta a shafinta na Facebook cewa; "ina tare da kai 'banana', kuma zamu kasance masu riko da gaskiya koda yaushe. Miji na bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel