Kotun koli tayi watsi da karar da aka shigar kan Sanata Aishatu

Kotun koli tayi watsi da karar da aka shigar kan Sanata Aishatu

Kotun koli tayi watsi da karar da aka shigar na neman soke zaben Sanata Aishatu Dahiru Ahmed (Binani) na mazabar Adamawa Ta Tsakiya.

Alkalai guda biyar ne suka amince da watsi da daukaka karar da dan takarar Abubakar Waziri ya yi na kallubalantar zaben Asihatu bayan ya janye karar.

A yayin yanke hukuncin, alkalan karkashin jagorancin Justice Mary Odili sun ce "Anyi watsi da karar duba da cewa wanda ya shigar da karar ya janye".

DUBA WANNAN: Cikar wa'adi: Sojoji sun farwa 'yan bindigan Zamfara, sun kashe 29

Waziri ya shigar da karar ne inda ya je kallubalantar zaben fidda gwani da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tayi da cewa Aishatu Ahmed ba ta cancanci yin takara a zaben ba.

A cikin karar da ya gabatarwa kotu ta bakin lauyansa, Muritala Abdulrasheed Waziri ya yi ikirarin cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ba ta sanar da su yin zaben ba kan lokaci wato kwanaki 21 kamar yadda doka ta tanada wanda hakan ya sabawa doka.

Sai dai lauya mai wakiltan Aishatu, Sam Ologun-Orisa (SAN) ya soki wanda ya shigar da karar saboda bata wa kotu lokaci.

A jiya Alhamis, Legit.ng ta ruwaito cewa kotun sauraron karrarkin zabe tayi watsi da bukatar da jam'iyyar Hope Democratic Party ta shigar na janye karar da ta shigar na kallubalantar nasarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben Fabrairun 2019.

A yayin yanke hukuncin, Alkalin Kotun Justice Mohammed Garba ya ce jam'iyyar HDP da dan takarar shugaban kasar ta Cif Ambrose Onwuru suna cikin jerin wadanda suka shigar da kara kan zaben a idon doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164