Hukuncin Kotu: APC Ba Za Ta Bari a Karbe Mulkin Jihar Nasarawa ba Inji Ganduje
- Abdullahi Umar Ganduje ya yi jawabi a liyafar da aka shiryawa Hon. Aliyu Bello a birnin Lafiya da ke jihar Nasarawa
- Aliyu Bello shi ne shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Nasarawa wanda ke fuskantar barazanar rasa mulki a kotu
- Shugaban APC na shiyyar, Muazu Rijau ya wakilci Ganduje, ya dauki alkawarin APC mai mulki ba za ta rasa jihar ba
Nasarawa - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin hana jam’iyyar adawa karbe iko da jihar Nasarawa.
Thi Day ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi wannan alkawari ne wajen gagarumar liyafar da aka shiryawa Hon. Aliyu Bello a lafiya.
Da yake jawabi a taron da aka yi domin girmama shugaban APC na rehen Nasarawa, Abdullahi Ganduje ya ce jam’iyyarsu ce ta lashe zaben 2023.
Muazu Rijau ya wakilci Abdullahi Ganduje
Shugaban APC na Arewa maso tsakiya, Alhaji Muazu Rijau ya wakilci Ganduje wajen taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Muazu Rijau yake cewa shakka babu jam’iyyar APC ce ta yi nasara a zaben gwamnan Nasarawa, kuma su na sa ran cigaba da mulki.
“Mun ci zabe, kuma za mu kare kujerarmu. Babu shakka a game da wannan. Nasarawa ta jam’iyyar APC ce, kuma APC ta jihar Nasarawa ce.
Mu ne ke rike da mulki kuma da yardar Ubangiji za mu cigaba da yin mulki."
- Muazu Rijau
An yabi Shugaban Jam'iyyar APC
The Nation ta ce Gwamna, Umaru Tanko Al-Makura da Sanata Ahmed Aliyu Wadada duk sun yabawa irin salon shugabancin Hon. Aliyu Bello.
Gwamna Sule ya ce shugaban na APC ya samar da shugabancin da jam’iyyarsu ta ke bukata duk da kotun karar zaben gwamna ta ba PDP gaskiya
"Jihar Nasarawa ba ta fara ganin cigaban kwarai ba sai a 2011 a lokacin zuwan tsohwar jam’iyyar CPC, wanda ta rike ta shiga APC.
A lokacin ne mu ka fara ganin wasu cigaba. Cigaba a bangaren ilmi, kiwon lafiya, gina hanyoyi da kuma sauran abubuwa na cigaba."
- Sanata Umaru Tanko Al-Makura
Jihohin PDP da APC da ake rikicin siyasa
Kamar yadda aka gani a lokacin Rochas Okorocha, kun ji labari Gwamnan Imo ya rabu da mataimakin shi ganin ya na neman tazarce.
Gwamnan Ondo ya na fada da mataimakinsa kamar yadda ta faru da tsohon mataimakinsa a 2019, hakan ya yamutsa siyasar jihar.
Asali: Legit.ng