Yan Jam’iyyar APC a Kano Sun Koka Kan Yadda Abba Gida Gida Ya Nuna Wariya a Rabon Kayan Tallafi
- Wasu ‘yan jam’iyar APC a Kano sun yi Allah wadai da yadda aka nuna wariya a rabon kayan tallafi a jihar
- A makon da ya gabata ne Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da rabon kayan abinci na rage radadi a jihar
- Masu korafin sun koka inda su ka ce masu jajayen kai kawai aka bai wa kayan abincin saboda siyasa
Jihar Kano – ‘Yan jam’iyyar APC a jihar Kano sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta nuna wariya kan rabon kayan abinci na tallafi.
A makon da ya gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon kayan tallafin abinci na masara da shinkafa na tallafi da Gwamnatin Tarayya ta bayar.
Meye mutane ke cewa kan tallafin Abba Kabir?
Sai dai wasu daga bangaren jam’iyyar adawa ta APC sun bayyana cewa rabon an yi tuwo na maina ne kawai wanda aka bai wa ‘yan jam’iyyar NNPP kadai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin Nasarawa, Usman Muhammad Maliya ya ce abin bai taka kara ya karyaba kuma akwai yaudara a cikin rabon da son kai.
Usman ya shaidawa DCL Hausa cewa:
“Irin kilo 10 din nan mai dauke da kwano uku kacal ne, wani buhun za ka ga an rubuta shinkafa amma masara ce a ciki.
“Kuma ba talakawan jihar Kano aka bai wa ba, iya mutane masu jan kai ‘yan jam’iyyar NNPP su kadai aka rabawa wannan shinkafa.”
Ya kara da cewa babu wani dan APC da ya samu wannan shinkafa duk wanda ka gaya samu to dan NNPP ne.
Wane martani hadimin Abba Kabir ya yi?
A bangarenshi, Shehu Isa Direba wanda dan jam’iyyar APC ne ya ce daman sun yi tsammanin haka daga gwamnatin.
Ya ce:
“Ba su yi duba da yadda Gwamnatin Tarayya ta aiko musu da wannan kudaden ba tare da duba su gwamnatin adawa ba ce a kasa, da an yi la’akari da haka da ba su samu ba.
“Gwamnatin Tarayya ba ta yi la’akari da su masu jajayen kai ba ne, abin da ya kamata su duba shi ne gwamnati ta sani idan kai mai mulki ne alhakin kowa na kanka.”
Hadimin Gwamna Abba ta bangaren ‘yan jarida, Shehu Haske ya ce tsarin da su ka bi talakawan Kano sun yi na’am da shi, inda ya ce masu wannan zargin mutane ne wadanda ba su da godiyar Allah.
Abba Kabir ya kaddamar da kayan abinci na tallafi
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da kayan rabon tallafin abinci don rage radadi na Gwamnatin Tarayya.
Abba, yayin kaddamar da tallafin ya gargadi jami’an tsaro da mambobin kwamitin kan taba kayan talakawa.
Asali: Legit.ng