Kotun Zabe: Kano, Nasarawa Da Sauran Jihohin Da APC, PDP da Labour Party Suka Yi Nasara
Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zama a jihohi 28 na kasar inda aka yi zaben gwamnoni ta yanke hukunci a jihohi 22, yayin da yanzu ake sa ran yanke hukunci kan sauran jihohi takwas kafin karshen watan Oktoba.
A gaba daya hukunci 22 da aka yanke zuwa yanzu, jam'iyyar PDP ta yi nasara a 11, APC ta yi nasara a 10, yayin da LP ta yi nasara a jiha daya.
Kamar yadda dokar zaben 2022 ta tanadar, ana sa ran kotunan zabe su saurara tare da yanke hukuncinsu cikin kwanaki 180, kuma tuni yawancinsu suka yi kokarin aiki da lokaci.
Jerin gwamnonin da kotun zabe ta tsige
Zuwa yanzu, kotunan zabe sun tsige akalla manyan gwamnoni biyu. Na farko ya kasance Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP daga jihar Kano, wanda kotu ta tsige shi bayan ta tsame takardun kuri'u marasa inganci sannan ta ayyana shi a matsayin wanda ya zo na biyu a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan sai kotun ta ayyana dan takarar APC, Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris a jihar Kano bayan an sake kirga kuri'un.
Haka kuma, kotun zaben gwamna da ke zama a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, ta tsige Gwamna Abdullahi Sule na APC sannan ta ayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai kuma Gwamna Sule da Abba Gida Gida sun yi watsi da hukuncin kotun zaben sannan sun sha alwashin daukaka kara a cikin lokaci.
Yadda PDP, APC da Labour Party suka yi nasara a kotunan zabe
Ga jerin yadda suka yi nasara a kotunan a kasa:
S/N | PDP | APC | Labour Party |
1 | Filato | Gombe | Abia |
2 | Zamfara | Cross River | |
3 | Bauchi | Benue | |
4 | Enugu | Lagas | |
5 | Nasarawa | Kano | |
6 | Delta | Ogun | |
7 | Akwa Ibom | Ebonyi | |
8 | Oyo | Kaduna | |
9 | Taraba | Kebbi | |
10 | Adamawa | Sakkwato | |
11 | Ribas |
INEC ta yi amai ta lashe, ta musanta zare hannu a daukaka kara kan zaben gwamnan Kano
A wani labarin kuma, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sake daukaka kararta kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.
Hakan na zuwa ne yan awanni bayan hukumar zaben, a cikin wata wasika da ta aike daga hedkwatarta, ta sanar da muradinta na janye karar.
Asali: Legit.ng