Dan Majalisar Tarayya Na Jam'iyyar NNPP A Kano Ya Yi Nasarar Dawo Da Kujerarsa A Kotun Daukaka Kara

Dan Majalisar Tarayya Na Jam'iyyar NNPP A Kano Ya Yi Nasarar Dawo Da Kujerarsa A Kotun Daukaka Kara

  • Kotun koli ta dawo da kujerar dan majalisa a jihar Kano bayan rasa kujerarsa a watan Agusta
  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Tarauni, Mukhtar Yarima ya yi nasara ne a kotun kolin ne bayan ta yi fatali da hukuncin kotun kararrakin zaben
  • A watan Agusta ne kotun sauraran kararrakin zabe ta kwace kujerar dan majalisar kan zargin takardun bogi

Jihar Kano - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Tarauni a majalisar Tarayya, Mukhtar Umar Yarima ya yi nasarar kwato kujerarsa a kotun daukaka kara.

A watan Agusta ne kotun kararrakin zabe ta kwace kujerar dan majalisar a jihar Kano wanda dan jam'iyyar NNPP ce mai mulki a jihar.

Dan majalisa a Kano ya kwato kujerarsa a kotun daukaka kara bayan rasa ta
Dan Majalisar NNPP A Kano Ya Yi Nasarar Dawo Da Kujerarsa. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

Wane hukuncin kotun ta yanke kan majalisar Kano?

Alkalin kotun, I. P Chima ya rusa zaben Yerima kan zargin mika takardar bogi na kammala firamare ga hukumar zabe ta INEC, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yerima ya musanta zarginshi da ake kan mika takardun bogi na makarantar firamare ga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC kafin zaben da aka gudanar a wannan shekara.

Ya ce matsalar takardar kawai sauyin suna ne kuma ta hanyar da ya dace aka yi wanda hakan ta faru tun kafin zaben 2023.

Wane mataki dan majalisar ya dauka a Kano?

Amma kotun kolin a yau Asabar 7 ga watan Oktoba ta yi watsi da hukuncin kotun inda ta ce ba ta da kwakkwaran hujja kan takardun bogin.

Kotun har ila yau, ta tabbatar da Hafizu Kawu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Faburairu, Daily Trust ta tattaro.

Bayan yanke hukuncin kotun, Yerima ya garzaya kotun daukaka kara don kwato kujerarsa da ya ke ganin an kwace cikin rashin adalci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Ya Bayyana Dan Najeriya Da Ya Karfafa Masa Gwiwa Ya Binciki Tarkardun Tinubu

Kotu ta kwace kujerar Abba Gida Gida a Kano

A wani labarin, kotun sauraran kararrakin zaben a jihar Kano ta rusa nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP kan kura-kurai da dama.

Kotun ta kuma tabbatar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashen zaben da aka gudanar a watan Maris.

Gawuna dai na kalubalantar zaben Abba Kabir da cewa an tafka mummunan magudi da aringizon kuri'u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel