Manyan kiristocin CAN sun kori shugaban da ya taya Dr Pantami murnar zama farfesa
- Kungiyar CAN ta kori shugabanta na jihar Gombe biyo bayan taya Dr Pantami murnar zama farfesa
- Kungiyar CAN ta ce shugaban na Gombe ya yi katsalandan da shiga hurumin da bai kai ba a yanzu
- Bisa wannan, CAN ta kore shi tare da bashi shawarin yadda shugabanci yake musamman a kungiyar
Kungiyar CAN ta aike da sakon dakatarwa ga shugaban riko na kungiyar reshen jihar Gombe bayan da ya taya ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Ibrahim murna haye matsayin farfesa a makon jiya.
CAN ta bayyana cewa, taya murnar da shugaban na reshen jihar Gombe ya yi ya jawo cece-kuce tsakanin mambobin kungiyar, lamarin da ya kai ga tunzura su.
A cikin wasikar kora da Legit.ng Hausa ta samo, wacce aka aikewa shugaban na CAN dauke da sa hannun Babban Sakataren kungiyar Barista Daramola Joseph Bade da kwanan wata 15 ga watan Satumba, ta bayyana dalilan da suka jawo korar.
A cewar wasikar:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Biyo bayan sakon taya murna ga ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, muna rubuta maka don sanar da kai cewa, aikinka ya jawo cece-kuce da yawa daga cikin membobin Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN)."
Bayan bayyana gargadi ga shugaban, kungiyar CAN ta karashe batun ta da bayyana korarsa da kuma umartarsa da ya mika abubuwan da mallakin CAN ne ga wanda zai karbe shi.
Kana sun shawarce shi da cewa:
"Nan gaba, an shawarce ka da ka nemi shawara da neman yarda daga ikon kasa don MU IYA MAGANA DA MURYA DAYA"
'Kungiyar Kiristocin Nigeria, CAN, ta jinjinawa Pantami: Muna alfahari da kai a matsayin ɗan mu
A wani labarin, Kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Gombe ta kira ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami da dan ta, SaharaReporters ta ruwaito.
Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara
A cikin wata wasika wacce sakataren kungiyar, Senior Apostle John Adedigba ya sanya hannu a madadin duk sauran ‘yan kungiyar ya kira Pantami da dan su.
Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, kungiyar kiristocin Najeriya ta reshen jihar Gombe ta taya ministan sadarwa, Isa Ali Pantami farin cikin samun karin girma zuwa farfesa a harkar tsaron yanar gizo.
Asali: Legit.ng