Jam'iyyar NNPP Ta Ce Tinubu Ya Yi Kuskuren Zaben Ganduje A Matsayin Shugaban APC
- Shugaban jam'iyyar NNPP a Kano, Hamisu Dungurawa ya soki zaban Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC
- Dungurawa ya ce Ganduje bai taba samun nasara ba a baya inda ya ce dukkan nasarorinshi sun ta'allaka da Kwankwaso
- Dungurawa ya bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Oktoba ga manema labarai a Kano
Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta bayyana cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi kadan ya kawo nasara a zabukan jihohin Kogi da Imo.
Shugaban jam'iyyar a jihar, Hashimu Dungurawa shi ya bayyana haka a yau Asabar 7 ga watan Oktoba a Kano.
Meye NNPP ta ce kan shugabancin Ganduje a APC?
Dungurawa ya ce samun shugabancin APC na Ganduje kawai an rasa wanda za a zaba aka bashi, Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hashimu wanda ya taba zama hadimin Ganduje ya ce ya san Ganduje tuntuni a matsayin wanda ba ya nasara a duk abin da ya saka a gaba.
Ya ce:
"Abubuwa da dama sun faru a siyasa, mu na magana ne kan mutumin da ba ya iya cin zabe a baya gida da waje.
"Ganduje ya gagara kawo jihar Edo a zaben da ya gabata kuma ya dawo Kano inda ya bugu a zaben da aka gabatar na 2023.
"Babban kuskure da Shugaba Tinubu ya yi shi ne zaban Ganduje a matsayin shugaban APC, mutumin da ba zai iya sauya komai ba yayin da ake bukatar nasara."
Wane sako NNPP ta tura wa Ganduje da APC?
Dungurawa ya kara da cewa zaben da za a gudanar a jihohin Kogi da Imo za su tabbatar da luskuren Tinubu na zaban Ganduje wannan matsayi.
Shugabannin Jam'iyya 21 da Jiga-Jigai Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Arewa, Sun Faɗi Abinda Ya Ja Hankalinsu
Ya ce dukkan nasarorin da Ganduje ya samu sun ta'allaka ne da Kwankwaso wanda dole ya dawo gare shi idan ya na son tsayuwa da kafafunsa, Thisday ta tattaro.
Ganduje ya kafa kwamitin kamfe a Imo
A wani labarin, Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin kamfe a jihar Imo.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zabuka a jihohin Kogi da Imo a ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Asali: Legit.ng