Zaben Kogi: Shugabanni LP Na Kananan Hukumomi 21 Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Zaben Kogi: Shugabanni LP Na Kananan Hukumomi 21 Sun Sauya Sheka Zuwa APC

  • Jam'iyyar LP ta kama hanyar rushewa yayin da shugabanninta na ƙananan hukumomi 21 suka sauya sheƙa zuwa APC a jihar Kogi
  • Jiga-Jigan sun bayyana cewa sun gamsu da cancantar ɗan takarar APC a zaben gwamna mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023
  • Shugaban APC na jihar, Abdullahi Bello, wanda ya tarbe su, ya nuna farin ciki bisa matakin da suka ɗauka

Jihar Kogi - Jam'iyyar Labour Party (LP) ta gamu da gagarumin cikas yayin da shugabanninta na rassan kananan hukumomi 21 suka sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Kogi.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa shugabannin LP sun koma APC ne tare da ɗumbin magoya bayansu ranar Jumu'a 6 ga watan Oktoba, 2023.

Jigan-jigan LP sun koma APC.
Zaben Kogi: Shugabanni LP Na Kananan Hukumomi 21 Sun Sauya Sheka Zuwa APC Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Bello, shi ne ya tarbi wadanda suka sauya shekar hannu bibbiyu a Lugard House dake Lokoja.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala 1 Da Aka Gano Bayan Taron da Atiku Ya Gudanar Kan Shugaba Tinubu a Abuja

Jagoran masu sauya shekar, Awe Kayode, ya ce sun yanke shawarar ruguza tsarinsu ne zuwa APC domin goyon bayan dan takarar gwamnan, Usman Ododo, a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa suka zaɓi sauya sheka zuwa APC?

Kayode ya kuma ce sauya shekar tasu ya zama tilas ne a daidai lokacin da suka fahimci cewa jam’iyyar LP ta rasa madafa a jihar Kogi.

Ya ce:

“Wani dalilin da ya sa muka sauya sheka shi ne mun gamsu cewa dan takarar APC, Usman Ododo, yana da kishin ƙasar da ake buƙata don ɗora wa daga kan nasarorin da Gwamna Yahaya Bello ya samu."
“Ni ɗan APC ne kafin na koma LP, yau gani na dawo tare da ƙarin mutane kuma mun shirya tsaf don ƙara bunƙasa jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Mata da Miji da 'Ya'yansu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki Mai Ƙarfi a Jihar Arewa

Jam'iyyar APC ta musu maraba

Da yake karbar masu sauya sheka, Shugaban APC na Kogi, Abdullahi Bello, ya ce “APC jam’iyya ce da ta yi imani da ci gaba, daidaito da kuma tsarin kyautata wa wanda ya mata bauta."

Bello, ya tabbatar wa sabbin mambobin jam’iyyar cewa za su ci moriyar duk wani gata da alfarma daidai da matsayin sauran tsoffin 'ya'yan jam’iyyar APC, Dailypost ta tattaro.

Ya kara da cewa ya yi farin ciki da cewa wadanda suka sauya sheka suna da kishi kuma suna da hankalin iya banbance tsakanin daidai da kuskure.

Bamu da Shirin Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya In Ji NNPCL

A wani rahoton na daban kuma Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya musanta rahoton cewa farashin fetur zai ƙara tashi a faɗin Najeriya.

A wata sanarwa da mahukuntan NNPCL suka fitar ranar Jumu'a, sun ce kamfanin ba shi niyyar ƙara tsadar mai.

Kara karanta wannan

Muhimmin Dalilin da Ya Sa Na Jagoranci Tawagar NWC Muka Je Wurin Buhari a Daura, Ganduje Ya Magantu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262